'Allah ba zai Bari ba,' Jigon APC Ya Yi Gargadi kan Adawa da Tinubu
- Jigo a jam’iyyar APC, Obidike Chukwuebuka, ya ce shugaba Bola Tinubu ya ba matasa dama ta hanyar raba mukamai
- Obidike Chukwuebuka ya bayyana cewa Allah ba zai yafe wa matasan da suka yi adawa da gwamnatin Tinubu ba
- Matashin ya ambaci wasu ayyukan da ya ce an yi wa matasan Najeriya karkashin Tinubu a matsayin hujjojinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Wani jigo a jam’iyyar APC, Obidike Chukwuebuka, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ya inganta rayuwar matasa a Najeriya ta hanyar daukar matakai da manufofi masu kyau.
Obidike, wanda shi ne shugaban kamfanin mai na Bidiks, ya ce zai zama babban kuskure kuma rashin kishin kasa idan matasa suka yi adawa da Tinubu da ke nuna kulawa a gare su.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa ya ce Allah ba zai yarda da haka ba, domin shugabancin Tinubu ya mayar da hankali kan gina makomar matasa da kuma ci gaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Bola Tinubu ya yi wa matasa?
A cewar Obidike, Tinubu ya nuna bambanci da shugabannin baya ta hanyar bai wa matasa manyan mukamai a gwamnati.
Ya ambaci wasu daga cikinsu kamar ministar harkokin Matasa, Dr Jamila Bio Ibrahim, karamin ministan matasa, Ayodele Olawande.
Haka zalika ya ambaci shugaban hukumar NASENI, Khalil Halilu, shugaban FIRS, Zacch Adedeji, da kuma shugabar NSIPA, Delu Bulus Yakubu.
Ya ce wadannan mukaman ba wai na nuna alfarma ba ne, illa dai dama ce da aka bai wa matasa don su jagoranci manyan sassan tattalin arziki tare da kawo sababbin dabaru da tsari.

Source: Twitter
Jigon APC ya fadi manufofin Tinubu
Obidike ya kuma jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta kafa manufofi masu tasiri wajen karfafa matasa.
Ya ce daga ciki akwai shirin bayar da bashi ga dalibai wadda zai taimaka wa masu karatu su ci gaba ba tare da matsalar kudi ba.
Haka kuma ya ce akwai shirin 3MTT da zai horar da matasa miliyan 3 a fannin kimiyya da fasahar zamani nan da shekarar 2027.
Wannan, a cewarsa, ya nuna cewa gwamnati na gina wata sabuwar kasa da matasa za su jagoranta.
Kiran Chukwu ga matasan Najeriya
Obidike ya bukaci matasa su ci gaba da nuna kishin kasa tare da gujewa siyasar ruɗu da ya ce wasu ke kokarin amfani da ita wajen raba kawunan jama’a.
Daily Post ta wallafa cewa ya yi gargadin cewa duk wanda ya yi adawa da manufofin shugaba Tinubu yana aiki da abokan gaba masu son hana cigaba.
A cewarsa:
“Shugaba Tinubu yana ginawa matasa makoma inda za su iya shugabanci, yin kasuwanci da inganta fasaha.
"Idan ka yi adawa da wannan shiri, ka yi adawa da makomar matasanmu, kuma Allah ba zai yafe maka ba.”
Legit ta tattauna da wani matashi
Legit Hausa ta tattauna da wani matashi mai aikin kafinta, Abdulhakim Hussaini kan maganar da Chukwu ya yi.
Abdulhakim ya ce:
"Har yanzu shugaban kasa bai gama sallamar matasa ba, ya kamata a ba mu jari domin inganta sana'ar mu."
"Raba mukamai da bayar da horo ba su shafi masu sana'ar hannu da masu neman jari ba."
Dalilin cigaba da ciwo bashi a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kare matakin cigaba da ciwo bashi.
Shugaban FIRS, Zacch Adedeji ya bayyana cewa ciwo bashi ba wata matsala ba ce domin kasashe da dama suna cinsa.
Adedeji ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnatin Tinubu tana karbo kudi ne domin ayyuka ba biyan albashi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


