'Najeriya ba Legas ba ce,' ADC Ta Fadi abin da Ke Shirin Faruwa da Tinubu a 2027
- Jam’iyyar ADC ta ce mulkin Shugaba Bola Tinubu zai kare a 2027, tana gargadi kan yunkurin tsawaita mulki har zuwa 2031
- Kakakin jam’iyyar, Mallam Bolaji Abdullahi, ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa a magance tsaro, yunwa, da tsadar rayuwa
- A cewar ADC, ya kamata Shugaba Tinubu ya fara shirin fita daga fadar Aso Rock Villa a 2027 idan har ya damu da 'yan kasar nan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Jam’iyyar adawa ta ADC ta yi watsi da tabbacin da fadar shugaban kasa ta bayar cewa Shugaba Bola Tinubu ba ya da niyyar tsawaita wa’adinsa bayan shekarar 2031.
A cewar jam’iyyar, kundin tsarin mulki ya fayyace cewa mulkin shugaban ƙasa zai ƙare a shekarar 2027, don haka ta yi gargaɗi kan duk wani yunƙuri na tsawaita wa’adi.

Source: Twitter
ADC ba ta yarda da karin wa'adin Tinubu ba
A cikin wata sanarwa da kakakin jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya sanyawa hannu, ADC ta ce ‘yan Najeriya ba za su so a tsawaita mulkin Tinubu da ko kwana ɗaya ba, inji rahoton Vanguard.
Ya zargi gwamnatin Tinubu da gazawa wajen tabbatar da tsaro, yaƙi da yunwa da talauci, da kuma durkusar da darajar tsarin mulki ta hanyar amfani da iko fiye da kima.
“Ya kamata shugaban ƙasa ya fara shirin barin ofis a shekarar 2027, saboda yawan satar mutane da kashe-kashe da ke ƙara yawaita a ƙasar nan, tsadar rayuwa da yunwa, haraji masu nauyi da kuma cin karfin iko da ba a taɓa gani ba, in har yana da gaskiya
“Duk wani yunkuri na tsayawa takara bayan wannan wa'adi zai tabbatar da cewa wannan gwamnati ba ta sani ba ko ba ta damu da abinda jama’a ke ji ba."
ADC ta zargi Tinubu da kin son barin mulki
Sanarwar ADC ta biyo bayan kalaman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya zargi Tinubu da son zama shugaban kasa na har abada.
Bayan fadar shugaban ƙasa ta karyata wannan ikirari, ADC ta ce hakan ya nuna cewa akwai kamshin gaskiya a zancen El-Rufai, inji rahoton Daily Trust.
“Amsar da fadar shugaban ƙasa ta bayar kan kalaman El-Rufai ta tabbatar da abin da ‘yan Najeriya suka dade suna zargi: wannan gwamnati ta fita daga sha'anin jama’a gaba ɗaya.
“Maganar cewa zai ci gaba da mulki har zuwa 2031 na nuna cewa ya ɗauki tazarcensa a matsayin 'tilas', ba tare da ya cancanci hakan ba. Amma har yanzu Tinubu bai nuna cewa ya cancanci wa’adi na biyu ba."
- Mallam Bolaji Abdullahi.
“Yan bindiga sun daina jin tsoro” – ADC

Source: Facebook
A kan harkar tsaro, ADC ta ce ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane sun mamaye wasu yankuna na Arewa, suna ayyukansu ba tare da fargaba ba.
“'Yan bindiga, masu garkuwa da mutane yanzu suna tafiyar da harkokinsu ba tare da wata fargaba ba. Ana sace jama’a a tsakar rana. Kauyuka sun koma filayen yaƙi.
- Mallam Bolaji Abdullahi.
A kan tattalin arziki, jam’iyyar ta soki gwamnatin Tinubu da cewa ta lalata Naira, ta ƙara hauhawar farashin kaya, ta rusa kasuwanci da kuma kakaba talauci.
El-Rufai ya gargadi 'yan Najeriya kan Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake yin kalamai masu kaushi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
El-Rufai ya yi gargadin cewa gwamnatin Tinubu ta kama hanyar mulkin kama-karya duba da yadda ake tafiyar da ita a yanzu, ba tare da la'akari da halin da kasa ke ciki ba.
Ya bukaci 'yan Najeriya da su yi kokarin ganin cewa sun raba Tinubu da mulkin Najeriya a zaben shekarar 2027, tun ana girma da arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


