Sanata Natasha Ta Isa Majalisar Dattawa Tare da Dandazon Magoya Baya, An Tarwatsa Su

Sanata Natasha Ta Isa Majalisar Dattawa Tare da Dandazon Magoya Baya, An Tarwatsa Su

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta koma bakin aiki yau Talata, 23 ga watan Satumba, 2025
  • Natasha tare da magoya bayanta sun isa kofar shiga zauren Majalisar Dattawa amma jami'an tsaro suka hana mutane shiga
  • Wannan na zuwa ne bayan Majalisa ta bude ofishin Sanata Natasha wacce aka dakatar na tsawon watanni shida, tare da ba ta izinin komawa ofis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Sanata Mai Wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta isa ofishin ta da ke harabar Majalisar Dattawan Najeriya a Abuja yau Talata, 23 ga watan Satumba, 2025.

Sanata Natasha ta dura ofishinta ne sa'o'i kalilan bayan Majalisa ta bude ofis din a wani bangaren shirye-shiryen komawarta bakin aiki.

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Hoton Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan a ofishinta na Majalisar Dattawa Hoto: Natasha Akpoti-Uduaghan
Source: Facebook

Rahoton jaridar Leadership ya tattaro cewa Natasha, wacce Majalisar Dattawa da dakatar na tsawon watanni shida, na shirin komawa aiki da zaran hutun sanatoci ya kare.

Kara karanta wannan

Duk da ta koma ofis, Natasha ta ki yin shiru, ta sake bankado wani laifin Akpabio

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan ta isa ofis, Sanatar Kogi ta Tsakiya ta jaddada cewa tana nan kan bakarta cewa ba za ta bai wa Majalisar Dattawa hakuri ba.

An bude ofishin Sanata Natasha a Majalisa

Tun da farko, Majalisar Tarayya ta buɗe ofishin Sanatar Kogi ta Tsakiya da ke Suite 2.05 a ɓangaren Majalisar Dattawa.

'Yar Majalisar Dattawan ta isa ofishinta tare da dandazon magoya baya, wadanda suka rako ta domin murnar komawarta bakin aiki.

Sai dai rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa jami'an tsaro sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa mutane amma sun bar Sanata Natasha ta shiga ofis.

Jami'an tsaro sun tarwatsa magoya baya

Shaidu sun bayyana lamarin a matsayin mai matuƙar tashin hankali, inda suka nuna bacin ransu kan yawan jami’an tsaro da aka tura wurin, da yadda suka tarwatsa taron magoya bayan Natasha.

Daga baya jami’an agajin gaggawa suka kwashe wasu daga cikin waɗanda suka ji rauni, yayin da ma’aikata da ‘yan majalisa suka nuna damuwa game da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Rigima za ta kare: Majalisar dattawa ta bude ofishin Natasha bayan wata 6

“Ya kamata wannan dawowa ta kasance mai cike da tarihi a gare ta, amma ya koma abu mara dadi,” in ji wani ma’aikacin Majalisar Tarayya.
Sanata Natasha.
Hoton Sanata Natasha lokacin da ta isa ofishinta a Majalisar Dattawa Hoto: Natasha Akpoti
Source: Facebook

Sanata Natasha ta nuna bacin ranta

Da take mayar da martani, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi tir da yadda aka tarwatsa magoya bayanta, tana mai cewa ya kamata a daraja dawowarta bisa tsarin dimokuraɗiyya.

“Wannan mutane ne ‘yan Najeriya da ba su aikata laifin komai ba, sun zo cikin zaman lafiya da murna; sun cancanci a mutunta su,” in ji Natasha.

Kungiyoyin mata sun kai kara UN

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyoyin kare ’yancin mata a Najeriya sun kai ƙara ga Majalisar Dinkin Duniya (UN) kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Gamayyar kungiyoyin matan sun zargi Majalisar Dattawa da nuna wa Sanata Natasha wariya da kuma kin yiwa kotu biyayya.

Kungiyoyin sun yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta matsa wa gwamnatin Najeriya da majalisar dattawa wajen bin hukuncin kotu da kuma kare lafiyar Natasha.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262