'Dan Majalisa Ya Shawarci Atiku, Peter Obi kan Takara da Tinubu a 2027
- Ana ci gaba maganganu kan batun tazarcen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, duk da cewa bai fito ya ce zai nema ba
- Wani dan majalisar wakilai daga jihar Legas, Dr. Wale Ahmed ya shawarci 'yan adawa kan ka da au fafata da Mai girma Tinubu a zaben 2027
- 'Dan majalisar ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya cancanci ya yi wa'adin mulki biyu yana jan ragamar kasar nan kamar yadda marigayi Muhammadu Buhari ya yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Agege, Dr. Wale Ahmed, ya ba da shawara ga Atiku Abubakar da Peter Obi kan kalubalantar Shugaba Bola Tinubu.
'Dan majalisar ya bukaci su daina shirin kalubalantar shugaban kasa a zaɓen 2027, yana mai jaddada cewa Shugaba Tinubu zai samu wa’adin mulki na biyu.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Agege a jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan adawa na neman kifar da Tinubu
Kalaman nasa na zuwa duk da cewa jam’iyyun adawa, ciki har da PDP, LP, NNPP sun yi alwashin kifar da Tinubu a zaɓen 2027.
Atiku Abubakar, Peter Obi, da kuma hadakar ADC karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, sun kasance a sahun gaba wajen sukar gwamnatin Tinubu.
'Dan majalisa ya magantu kan tazarcen Tinubu
Dr. Wale Ahmed ya kafa hujjar cewa tun da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari daga Arewa ya yi wa’adi biyu kan mulki, ya kamata adalci ya sa a bar Tinubu daga Kudu ya kammala nasa wa’adin na biyu.
Ya kara da cewa matakan sauye-sauyen tattalin arziki da Tinubu ya ɗauka, sun sanya Najeriya ta samu martaba da kafa tubalin murmurewar tattalin arzikinta na dogon lokaci.

Kara karanta wannan
Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027
"Dukkan abokan hamayyarsa su huta su bar shi ya yi wa’adi na biyu. Duk ’yan adawa su haɗa kai kawai su mara masa baya."
"Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari daga Arewa ya yi wa’adi biyu, don haka shi ma Tinubu ya kamata ya samu nasa wa’adin na biyu."
"Da ikon Allah, wa’adinsa na biyu tabbatacce ne. Zan wayar da kan al’ummata don tabbatar da cewa Tinubu ya koma mulki a karo na biyu."
- Dr. Wale Ahmed

Source: Facebook
Ɗan majalisar ya kuma kare cire tallafin mai, yana mai cewa matakin ya nuna jarumtar Tinubu da hangen nesan da yake da shi kan kasar nan.
Kungiya ta ba Atiku Abubakar shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiya mai suna, Save Democracy Mega Alliance (SDMA), ta mika kokon bararta ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar.
Kungiyar ta yi kira ga Atiku kan ya hakura da yin takara sannan ya marawa Peter Obi baya don ya zama shugaban kasa a zaben shekarar 2027.
Hakazalika, SDMA ta nuna cewa idan manyan 'yan siyasan suka yi takata a karkashin inuwar jam'iyyu daban-daban, ba za su iya kifar da Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
