'Ba da Mu ba,' NNPP Ta Nesanta Kanta da Shirin Kwankwaso na Shiga APC
- Sakataren tsagin NNPP, Dr Ogini Olaposi, ya ce shirin shiga APC na Rabiu Kwankwaso da Kwankwasiyya ne
- Olaposi ya bayyana cewa sun kori Kwankwaso da magoya bayansa daga jam’iyyar saboda cin amanar NNPP
- Ya ce jam’iyyar ta fara gyaran cikin gida domin shiryawa babban zaɓen 2027 bayan rikice-rikicen da suka yi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas - Tsagin Jam’iyyar NNPP ya yi karin haske kan maganar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta komawa jam’iyyar APC tare da magoya bayansa na Kwankwasiyya.
A cewar sakataren tsagin jam’iyyar, Dr Ogini Olaposi shirin ya shafi Kwankwaso da Kwankwasiyya ne kawai, ba jam’iyyar NNPP gaba ɗaya ba.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ya ce hakan ya tabbatar da cewa Kwankwaso ya rabu da NNPP tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olaposi ya jaddada cewa kowace tattaunawa da za a yi da Kwankwaso za a yi ta a matsayinsa na mutum ɗaya ne, ba a madadin jam’iyyar NNPP ba.
Shirin Kwankwaso na komawa APC
Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023 a ƙarƙashin NNPP, ya bayyana cewa shi da magoya bayansa za su iya komawa APC.
Sai dai ya gargadi cewa Kwankwasiyya ba za ta yarda a yi amfani da ita kawai don cin zaɓe a ajiye ta a baya ba.
Olaposi ya ce wannan furuci ya tabbatar da ikirarin NNPP cewa Kwankwaso da magoya bayansa tun da farko ba cikakkun mambobi ba ne.
Martanin NNPP kan rikicin cikin gida
Olaposi ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta sha wahala daga rikice-rikice da 'yan Kwankwasiyya ta jawo mata, tun bayan kammala zaɓen 2023.
A cewarsa, Rabiu Kwankwaso ya rasa jam’iyyar siyasa bayan ya nemi mamaye NNPP, amma ya gaza.
“Kwankwaso ba shi da jam’iyya. Ƙimar siyasarsa ta ragu bayan ya ci amanar NNPP da ta ba shi damar tsayawa takarar shugaban ƙasa,”
- In ji shi.
Ya ƙara da cewa mafi rinjayen magoya bayan Kwankwaso a Kano tun da dadewa sun koma APC, abin da ya nuna ƙarfin Kwankwasiyya ya ragu.

Source: Twitter
Batun yarjejeniya da Kwankwasiyya
Olaposi ya bayyana cewa yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin NNPP da Kwankwasiyya ta ƙare tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Daily Post ta wallafa cewa ya ce rikicin ya samo asali ne daga yunƙurin Kwankwasiyya na kwace ragamar jam’iyyar, maimakon su fice cikin lumana.
“Mun huta daga ƙalubalen su yanzu, kuma za mu ci gaba da shirya jam’iyya don babban zaɓe mai zuwa,”
- In ji shi.
Ya ce NNPP tana gyaran cikin gida don shirye-shiryen zaɓe a fadin ƙasar, bayan kammala babban taro da kotu ta amince da shi wanda ya samar da sabon shugabanci ƙarƙashin Dr Agbo Major.
Martani ga Kwankwaso kan shiga APC
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan Najeriya, musamman 'yan siyasa sun yi martani ga Rabiu Kwankwaso kan maganar shiga APC.
Hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya bayyana cewa suna maraba da Kwankwaso.
Wasu daga cikin mutane sun bayyana cewa bai dace ya koma APC ba, yayin da tsohon kwamishinan Kano, Muaz Magaji ya ce dama gidansa ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


