Atiku ko Tinubu: Kawunan Magoya bayan Buhari na CPC Ya Rabu a kan Zaben 2027
- 'Ya 'yan tsohuwar jam’iyyar CPC da marigayi Muhammadu Buhari ya kafa sun shiga rudani kan wanda za a mara wa baya a 2027
- Wasu tsofaffin shugabannin CPC sun kai ziyara ga Atiku, suna goyon bayan tsayawarsa takara a karkashin ADC a zabe mai zuwa
- Duk da hakan, wasu mutane 20 daga cikin tsofaffin shugabannin sun bayyana cikakken goyon bayansu ga APC ta ci gaba da mulki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – 'Ya'yan tsohuwar jam’iyyar CPC da mariga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa, ta shiga rikici kan zabe mai zuwa.
Kawuna sun rarrabu dangane da wanda za su mara wa baya a zaben shugaban kasa na 2027 — Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa tsohon Shugaba Buhari, wanda ya rasu a watan Yuli a wani asibiti da ke Landan, ya kasance ginshikin dunkulewar jam’iyyun CPC, ACN, ANPP.
Sauran jam'iyyun da aka hada kai wajen fatattakar PDP daga mulkin Najeriya sun hada da wani bangare na APGA da PDP, inda a shekarar 2013 da suka kafa APC.
An samu gibi a CPC bayan rasuwar Buhari
Bayan rasuwarsa, 'yan CPC suka shiga cikin rudani, inda wasu daga cikinsu suka bayyana goyon bayansu ga Atiku Abubakar, wasu kuma na tare da Bola Tinubu.
Daga cikin fitattun ‘yan CPC akwai: Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen; Tunde Bakare da tsohon gwamnan Nasarawa, Tanko Al-Makura.
Sauran sun hada da tsohon gwamnan Katsina, Aminu Masari, da kuma gwamnan jihar Katsina na yanzu, Dikko Umaru Radda.

Source: Facebook
A makon da ya gabata, Atiku ya karɓi bakuncin wasu tsofaffin shugabannin CPC a gidansa da ke Abuja, inda suka bayyana goyon bayansu ga tsayawarsa takara a 2027.
Atiku ya kuma wallafa bidiyon taron a shafinsa na X yana bayyana niyyar kafa sabuwar kawance da zai sauya mulkin Tinubu.
Tsagin CPC ya barranta kansa da Atiku
Sai dai, a wata sanarwa daga kungiyar tsofaffin Shugabannin jihohi na CPC, mai mutane 36 ta bayyana cewa 20 daga cikin su na tare da Tinubu yayin da 16 ke goyon bayan Atiku.
Shugabannin kungiyar sun ce akwai matsin lamba da kuma biyan kuɗi daga wasu ‘yan adawa da ya sa wasu 'ya'ayansu suka sauya sheka.
Kungiyar ta ce:
“Muna maida martani cewa mu 20 muna nan daram a APC. Ba za mu bar jam’iyyar da muka kafa tare da Buhari ba.”
Sun roƙi gwamnatin Tinubu da shugabancin APC da su daina wulakanta sashen CPC a cikin jam’iyyar don a gudu tare a tsira tare.
Mutanen Buhari na CPC sun gana da Atiku
A baya, mun wallafa cewa wasu daga cikin tsofaffin shugabannin tsohuwar jam’iyyar CPC sun kai ziyara ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a gidansa da ke Abuja.
Yayin ziyarar, sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 mai zuwa da fatan Atiku zai karbi ragamar kasar.
Wannan ganawa da aka yi a cikin makon nan ta kasance wata babbar alama ce ta fara kawance tsakanin wasu tsofaffin magoya bayan Buhari da Atiku a kan zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


