2027: Gangar Siyasa Ta Fara Kaɗawa, Sanata Ya Ƙaddamar da Kungiyar Zaɓen Tinubu

2027: Gangar Siyasa Ta Fara Kaɗawa, Sanata Ya Ƙaddamar da Kungiyar Zaɓen Tinubu

  • Sanata Gbenga Daniel ya ƙaddamar da ƙungiyar BATOGD domin yaƙin neman wa Shugaba Bola Tinubu kuri'a a zaɓen 2027
  • Ya ce shugaban ƙasa ya fara sabon salo na jagoranci da ke gyara tattalin arzikin ƙasa wanda ya sa dole a sake zabensa
  • Sanata Gbenga Daniel ya dage kan ƙoƙarin samar da jihar Ijebu, yana mai cewa dole ne a ba shi dama ya koma majalisa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun – Sanata mai wakiltar Ogun Gabas, kuma tsohon gwamnan jihar, Otunba Gbenga Daniel, nuna goyon bayansa ga 'tazarcen Bola Tinubu.'

Sanatan ya kuma kaddamar da wata ƙungiya mai suna BATOGD Movement, wacce za ta yi aiki a matsayin ƙungiyar tallafa wa sake zaɓen Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

2007: PDP ta bukaci Tinubu ya fara shirin mika mulki, ta kawo dalili

An fara yi wa Tinubu kamfen
Hoton Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Sanatan ya bayyana haka ne a wurin bikin ƙaddamar da babbar kasuwa da aka yi a Igode-Remo, karamar hukumar Sagamu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Daniel na son a sake zaɓen Tinubu

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Daniel ya yaba da jajircewar Tinubu wajen tunkarar ƙalubalen tattalin arziki da na zamantakewa da su ka addabi Najeriya.

Ya bayyana cewa idan aka sake zaɓen shugaban Kasar a 2027, Najeriya za ta ci gaba da samun ci gaba da bunƙasar da ake mora a yanzu.

Sanatan ya bayyana cewa ya kafa ƙungiyar BATOGD ne domin farfado buƙatar a sake zaɓen Tinubu ta hanyar nuna ayyukan da ya yi.

Sanata ya yi wa kansa kamfen 2027

Sanata Gbenga Daniel ya kuma bayyana cewa shi ne ya ɗauki nauyin kudurin kafa Hukumar cigaban Kudu maso Yamma da kuma ƙoƙarin samar da sabuwar jiha daga Ogun.

Daniel ya ce yana aiki kan ƙudurin samar da Jihar Ijebu, wanda zai kawo manyan fa’idoji ta fuskar raba kuɗin gwamnati, ayyukan yi da ci gaban yankin.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 4 da za su koma bakin aiki bayan janye dokar ta baci a Rivers

Tsohon Gwamnan Ogun na son komawa majalisa
Hoton Sanata Gbenga Daniel a wani zaman majalisa Hoto: @TheYemiKing
Source: Twitter

Ya bayyana cewa sama da Sanatoci 75 sun riga sun amince da shirin saboda haka akwai bukatar ya ci gaba da zama a majalisa.

A cewarsa, ta haka ne kawai zai tabbatar da nasarar ƙudurin kafa jihar, domin akwai hanyoyin musamman da ake bi wajen tura kudurori a majalisar

An yabi gwamnatin Tinubu

A nasa jawabin, Onigode na Igode, Oba Jamiu Sule-Onosipe, ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa gina babban kasuwar zamani a yankin.

Ya ce wannan aiki ya nuna jajircewar gwamnati wajen tallafa wa al’umman karkara da kuma tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.

Ya kara da cewa kasuwar za ta taimaka wajen rage asarar kayan gona, samar da riba ga manoma da ‘yan kasuwa, tare da ƙara ɗaukar ma’aikata a jihar Ogun.

El-Rufa'i ya gargadi jama'a kan Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa tshon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi kakkausar magana game da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

El-Rufai, wanda yana daga cikin waɗanda su ka yi fafutukar kafa gwamnatin nan, ya ce Tinubu ya fara tafiya ne kan turbar mulkin kama-karya a ƙasar nan.

Kwatanta mulkin Tinubu da na shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, inda ya ce ana ganin alamun daidai suke wajen tafiyar da mulkin da bai yi wa jama'a daɗi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng