El Rufai Ya Gargadi 'Yan Najeriya kan Tinubu, Ya Yi Hasashen Shirinsa kan Mulki
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake yin kalamai masu kaushi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- El-Rufai ya yi gargadin cewa gwamnatin Tinubu ta kama hanyar mulkin kama-karya duba da yadda ake tafiyar da ita
- Ya bukaci 'yan Najeriya da su yi kokarin ganin cewa sun raba Tinubu da mulkin Najeriya a zaben shekarar 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi gargadi kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
El-Rufai ya yi gargadin cewa gwamnatin Tinubu na tafiya zuwa mulkin kama-karya, inda ya kwatanta salon mulkinsa da na shugaban Kamaru, Paul Biya.

Source: Facebook
El-Rufai ya yi wannan jawabi ne a cikin wani bidiyo da aka sanya a shafin X, a daren ranar Asabar lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ziyarce shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya kai masa ziyarar goyon baya ne bayan harin da wasu “yan daba da ake zargin APC ta dauki nauyi suka kai masa” a wajen taron jam’iyyar ADC a Kaduna.
Me El-Rufai ya ce kan gwamnatin Tinubu?
A cikin jawabin nasa, El-Rufai ya bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin abin kunya ga akidun dimokuraɗiyya, yana zarginta da tattara iko a hannunta maimakon bin tsarin tarayya.
"Gaskiya ranka ya daɗe, a ganina abin kunya ne. Ina nufin yadda mutanen nan su ke abubuwa, yana nufin duk wadannan shekarun na cewa muna fada don dimokuradiyya da NADECO, da maganganun kare tsarin tarayya, duk ya zama shirme, karya ce kawai."
"Saboda wannan gwamnati (ta Tinubu) tana kokarin tattara dukkan iko a sama maimakon ta rarraba zuwa matakai na kasa.”
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya kara gargadin cewa idan ‘yan Najeriya ba su haɗu wuri guda don kawar da gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027 ba, akwai yiwuwar shugaban ya yi yunƙurin ci gaba da rike mulki irin na shugaban Kamaru, Paul Biya.
“Jimillar wannan shi ne muna fuskantar wani mummunan abin da bai taba faruwa a tarihin wannan kasa ba. Idan ba mu haɗu don kawo karshen gwamnatin Tinubu a 2027 ba, Tinubu zai yi yunƙurin zama Paul Biyan mu. Dukkan alamun suna nan, haka Paul Biya ya fara.”
- Nasir El-Rufai
El-Rufai ya yabawa Atiku
Yayin da yake yabawa bakonsa Atiku kan rawar da ya taka a fafutikar dimokuraɗiyya a Najeriya, El-Rufai ya ce ‘yan Najeriya suna dogaro da kwarewarsa da jagorancinsa wajen tattara jam’iyyun adawa.

Source: Twitter
“Kai (Atiku Abubakar) ne jagoranmu, ka taba jagorantar wannan gwagwarmaya a baya, ka yi yaki da mulkin soja, kana da kwarewa a tafiyar da dimokuraɗiyya."
"A lokacin da kai da Obasanjo kuka mulki kasar nan, babu wanda aka tsananta masa saboda ya yi ra’ayin siyasa daban, babu ko sau ɗaya."
"Har ma Shugaba Buhari, duk da kasancewarsa tsohon soja, bai taba yin hakan ba. Amma yanzu muna fuskantar cikakkun fararen hula, amma su ne mafi muni fiye da kowanne mulkin soja da muka taba yi.”
- Nasir El-Rufai
Matasan Arewa na son a binciki El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kungiyar matasan Arewa ta bukaci tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya mika kansa don a bincike shi.
Kungiyar ta bukaci El-Rufai ya bari a bincike shi kan yadda ya tafiyar da kudaden jihar Kaduna a lokacin mulkinsa.
Ta yi zargin cewa tsohon gwamnan ya ki yarda a bincike shi kan yadda ya gudanar da mulkinsa a Kaduna.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


