Malamai, Sarakuna da Wasu Jiga Jigai Sun Je Gidan Kwankwaso a Jihar Kano
- Malamai, masu unguwanni da jiga-jigan Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji sun kai ziyara gidan jagoran NNPP, Sanata Rabi'u Kwankwaso
- Wannan tawaga ta kai wa Kwankwaso ziyara har gida ne donin jaddada mubaya'a da goyon baya ga madugun Kwankwasiyya
- Ana ganin ziyarar ba za ta rasa nasaba da korar dan Majalisar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa daga jam'iyyar NNPP
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Limamai, dagattai da jagororin tafiyar Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebejii ta jihar Kano sun ziyarci jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso.
Malaman addinin Musulunci da sauran manyan kusoshin Kwankwasiyya a Bebeji sun gana da Kwankwaso a ziyarar da suka kai masa har gida yau Asabar.

Source: Twitter
Mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin midiya, Hon. Saifullahi Hassan ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X tare da hotuna.
Kwankwaso ya karbi bakuncin jiga-jigan NNPP
Ya ce jagoran NNPP ya karbi bakuncin wannan tawaga ne a gidansa da ke Miller Road a cikin birnin Kano yau Asabar, 20 ga watan Satumba, 2025.
Wannan na zuwa ne makonni kalilan bayan jam'iyyar NNPP ta kori dan Majalisa mai wakiltar Kiru da Bebeji a Majalisar Wakilai, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa.
Shugaban NNPP na Kano, Hashimi Dungurawa ya ce sun kori dan Majalisar ne bisa laifin cin amana da kuma rashin biyan hakkokin jam'iyya.
Limamai da dagattai sun je gidan Marigayi Buhari
Wannan mataki dai ya biyo bayan yadda Hon. Kofa ke yawan kai wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ziyara da kuma kalaman da ya fada cewa zai iya canza jam'iyya a duk lokacin da ya so.
Ana ganin wannan tawaga da ta kunshi malamai da masu rike da sarauta sun je gidan madugun ne domin tabbatar da cewa har yanzu karamar hukumar Bebeji na tare da shi.
Tawagar ta kara jaddada mubaya'a ga tsohon gwamnan na jihar Kano kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP a zaben 2023.

Source: Facebook
Abin da ya kai malamai gida Kwankwaso a Kano
Sanarwar da hadimin Kwankwaso, Saifullahi ya fitar ta ce:
"Jagoran Jam’iyyar NNPP na Kasa, Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD FNSE, ya karɓi bakukcin limamai, dagattai da magoya bayan Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji.
"Wannan tawaga ta ziyarci Kwankwaso ne domin tabbatar da cikakkiyar goyon bayansu ga tafiyar Kwankwasiyya a gidansa da ke titin Miller Road, Jihar Kano.
Kwankwaso ya gindaya sharadin shiga APC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Kwankwaso ya ce a shirye yake ya koma jam'iyyar APC amma biss sharadi.
Kwankwaso ya yi ikirarin cewa su ne suka tsaya suka fafata suka kuma gwagwarmaya wajen kafa jam’iyyar da ke mulki a yau, wato APC.
Ya bayar da tabbacin cewa, matuƙar aka tabbatar musu da kyakkyawar makoma a jam’iyyar APC, to za su sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki amma dai bisa wasu ka'idoji da sharudda.
Asali: Legit.ng

