Shugaba Tinubu Ya Samu Gagarumin Tagomashi yayin da Ake Tunkarar Zaben 2027
- Duk da bai bayyana aniyar yin tazarce ba, an yi wa Mai girma Bola Tinubu alkawarin miliyoyin kuri'u a zaben 2027
- Kungiyar Cagram wadda ta kunshi kungiyoyin goyon baya na APC, ta bayyana cewa ta gamsu da kamun ludayin mulkin Shugaba Tinubu
- Mataimakin shugaban kungiyar na kasa, ya yaba kan yadda ya kawo sauye-sauye masu amfani a fannin tattalin arzikin kasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ondo - Kungiyar Consolidated APC Grassroots Movement (CaGram) ta yi alkawarin kawo kuri'u ga Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Kungiyar ta yi alkawarin kawo kuri'un jama’a miliyan 10 kai tsaye don Shugaba Tinubu a zaɓen shugaban kasa na shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar The Nation ta kawo rahoto cewa mataimakin shugaban kungiyar CaGram na kasa, Hon. Agbi Stephen Omobamidele, ya bayyana hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Bola Tinubu ya samu yabo
Agbi Stephen Omobamidele wanda kuma shi ne mai ba da shawara na musamman kan harkokin jama'a ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa, ya yabawa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arzikin Tinubu a matsayin hangen nesan mai zurfi, wanda hakan ya zama daga cikin manyan dalilan da ya fi dacewa ya jagoranci Najeriya zuwa matakin ci gaba.
A cewarsa, tun bayan hawansa mulki, gwamnatin Tinubu ta aiwatar da muhimman matakai kamar dakatar da tallafin man fetur da wutar lantarki da kuma aiwatar da sauye-sauye a fannin haraji, waɗanda suka fara daidaita tattalin arzikin kasar nan.
"Hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya taɓa kai sama da kaso 34%, yanzu ya sauka kwarai zuwa kusan kaso 21.8% a tsakiyar 2025, yayin da kuɗaden ajiya na kasashen su ka wuce Dala biliyan 40."
"Shugaba Tinubu kuma ya ɗora babban buri na samun kaso 7% don bunkasar tattalin arziki a kowace shekara zuwa 2027, tare da babban shiri na ninka tattalin arzikin Najeriya har sau huɗu nan da shekarar 2030.”
"Waɗannan ba gwaje-gwaje ba ne, matakai ne domin farfado da tattalin arziki, kara kuɗin shiga, da karfafa ‘yan Najeriya."

Kara karanta wannan
'Za mu dora daga inda ya tsaya,' Anji abin da Tinubu ya fadawa iyalan Buhari a Kaduna
- Hon. Agbi Stephen Omobamidele

Source: Facebook
Yadda za a samarwa Tinubu kuri'u
Kungiyar CaGram ta kunshi fiye da kashi 70% na kungiyoyin goyon bayan APC da aka yi wa rajista tare da mambobi fiye da miliyan 1.2 a fadin kasa, rahoton jaridar Independent ya tabbatar da labarin.
Ta bayyana cewa an ɗorawa kowane mamba nauyin samar da akalla kuri’u 10 daga matakin kasa, abin da zai haifar da gagarumin tasiri a rumfunan zaɓe domin Shugaba Tinubu a 2027.
PDP ta ba Shugaba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya fara shirin yin bankwana da mulki.
Jam'iyyar ta bakin sakataren tsare-tsarenta na jihar Adamawa, ta shawarci Shugaba Tinubu ya fara shirin rubuta takardar mika mulki.
Hamza Madagali ya bayyana cewa 'yan Najeriya sun samu wayewar da ba za ta bari, su sake zabar Shugaba Tinubu a karo na biyu ba don jagorantar kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
