Kasa da Shekara 1 bayan Shan Kashi a Zabe, 'Dan Takarar Gwamnan PDP Ya Shirya Komawa APC
- 'Dan takarar gwamnan jihar Ondo a karkashin inuwar PDP, Hon. Agboola Ajayi, ya shirya raba gari da jam'iyyar
- Dukkan alamu sun nuna cewa Hon. Agboola Ajayi, zai sauya sheka ne zuwa jam'iyar APC mai mulki a jihar
- Matakin sauya shekar na zuwa ne bayan ya janye karar da ya shigar a gaban Kotun Koli kan sakamakon zaben gwamnan jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ondo - Dan takarar gwamnan jihar Ondo na jam'iyyar PDP, Hon. Agboola Ajayi na shirin komawa APC.
Hon. Agboola Ajayi zai koma jam'iyyar APC ne idan har ba wani sauyi aka samu ba.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta kawo rahoto kan batun sauya shekar tsohon dan takarar gwamnan a zaben ranar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Agboola Ajayi ya shirya barin PDP zuwa APC
Matakin Hon. Ajayi na sauya sheka ya biyo bayan janye karar da ya shigar a gaban Kotun Koli inda yake kalubalantar sakamakon zaɓen.
Ya bayyana cewa shawarar janye karar ta zo ne bayan ya yi shawarwari da iyalansa, abokan aikinsa, mambobin jam’iyya da kuma lauyoyinsa.
A cikin wata wasika da ya aikawa babban rajistaran Kotun Koli, tsohon mataimakin gwamnan ya ce matakin janye karar ya samo asali ne daga jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ingantaccen mulki.
"Bayan tattaunawa mai zurfi, mun cimma matsaya cewa a janye karar, kuma na yi hakan a hukumance."
"Bayan na yi aiki a matsayin mataimakin gwamna da kuma ɗan majalisa, babban burina shi ne nagartaccen shugabanci da zaman lafiya a Ondo da Najeriya."
Hon. Agboola Ajayi
Me Gwamna Aiyedatiwa ya ce?
A martaninsa yayin wata hira da tashar Channels tv, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa Ajayi ya riga ya nuna shirinsa na shiga APC domin goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu.
"Maganar gaskiya, Hon. Agboola Ajayi ya faɗa min da bakinsa cewa zai shiga APC. Ina jiran shi domin mu haɗa kai wajen gina jihar Ondo."
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa

Source: Facebook
Gwamnan ya kara bayyana hukuncin Kotun Koli na watsar da duk kararrakin da jam’iyyun adawa suka shigar a kan nasararsa a matsayin tabbacin karshe na sahihancin ragamar shugabanci da jama’ar Ondo su ka ba shi.
Hon. Agboola Ajayi, wanda ya tsaya takarar gwamna tare da wasu ‘yan takara 14, ya fito a matsayin babban abokin hamayyar Aiyedatiwa inda ya samu 117,845 kuri’u, yayin da ɗan takarar APC ya samu 366,781
Masu sharhi kan siyasa sun nuna cewa idan sauya shekar da ake sa ran Ajayi zai yi ta tabbata, za ta kawo sauyi a jihar Ondo.
Tsohon dan takarar gwamnan Ondo ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Ondo na jam'iyyar SDP, Otunba Bamidele Akingboye, ya yi bankwana da duniya.
Marigayin wanda ya yi takara a zaben gwamnan Ondo na shekarar 2024, ya rasu ne yana da shekara 60 a duniya.
Otunba BamideleAkingboye ya rasu ne a cikin gidansa da ke jihar Legas a ranar, 3 ga watan Satumban 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

