Abin da Gwamna Fubara Ya Fada kan Tinubu da Wike a Jawabinsa na Farko a Ribas

Abin da Gwamna Fubara Ya Fada kan Tinubu da Wike a Jawabinsa na Farko a Ribas

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya koma kan mulki bayan karewar watanni shida na dokar ta bacin da aka sanya a jihar Ribas
  • A jawabinsa na farko bayan ya shiga gidan gwamnati a Fatakwal, Fubara ya tuna da Bola Ahmed Tinubu da ubangidansa, Nyesom Wike
  • Fubara ya jaddada muhimmancin hadin kai, sulhu da kwanciyar hankali, ya na mai cewa zaman lafiya ya fi zama dan Sarki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya mika godiya ga Shugaban Kasa, Bola Tinubu da Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike.

Gwamna Fubara ya gode wa jagororin biyu ne bisa rawar da suka taka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Ribas.

Gwamna Siminalayi Fubara.
Hoton Gwamna Fubara yayin da yake jawabi kai tsaye bayan ya koma kan mulki a Ribas Hoto: @SimFubaraKSC
Source: Twitter

Fubara ya yi wannan jawabi ne yayin da yake magana da magoya bayansa a fadar gwamnatin jihar da ke Fatakwal a ranar Juma’a, in ji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Bayan ya koma mulki, an ji dalilin Gwamna Fubara na amincewa da dokar ta baci a Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan dai na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya cire dokar ta bacin da ya sanya a jihar tare da maida Fubara kan kujerarsa ta gwamna.

Magoya baya sun yi murna da dawowar Fubara

Dandazon magoya baya sun tarbi Mai Girma Fubara cikin murna da farin ciki lokacin da ya isa gidan gwamnati da ke Fatakwal a karon farko bayan watanni shida, in ji rahoton Daily Trust.

Da yake jawabi, Gwamna Fubara ya gode musu da al’ummar Jihar Ribas baki ɗaya saboda jajircewarsu da goyon bayan da suka nuna masa a lokacin da aka dakatar da shi.

“Ina godiya ga kowa da kowa da ya bayar da gudummawa wajen dawo da zaman lafiya a Jihar Ribas. Na san kowa yana son jin abin da zan fada," in ji shi.

Fubara ya gode wa Bola Tinubu da Wike

Yayin da yake nuna jin daɗinsa da godiya ga Shugaba Tinubu da tsohon gwamna Nyesom Wike, Fubara ya danganta su da nasarar dawo da kwanciyar hankali a jihar.

Kara karanta wannan

Wike ya fadi abin da ƴan siyasar Ribas suka saka a gaba bayan dawowar Fubara

“Ina gode wa ubanmu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, bisa yadda ya shiga tsakani kuma ya jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu.
"Haka kuma, ina mika godiyata ga jagoranmu, Mai Girma Nyesom Ezenwo Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya, saboda jajircewarsa wajen kawo ƙarshen wannan rikicin siyasa cikin gaggawa."

- In ji Gwamna Fubara.

Gwamna Fubara, Tinubu da Wike.
Hoton Shugaba Tinubu tare da Gwamna Fubara da Wike Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Gwamnan Ribas ya ja hankalin jama'a

Yayin da yake jaddada muhimmancin haɗin kai da sulhu, Fubara ya ce:

“Har yanzu akwai damar gyare-gyare, sulhu, da haɗin kai. Mu tuna da karin magana cewa: Zaman lafiya ya fi zama dan Sarki.
“Wannan lokaci ne da za mu sake farawa. Mu yi aiki tare cikin fata da ƙudurin gina Jihar Ribas da zaman lafiya, tare da tabbatar da cewa babu wanda aka bari a baya."

Majalisar Dokokin Ribas ta koma bakin aiki

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Dokokin Ribas ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kuɗin jihar a lokacin mulkin riko na wata shida.

Majalisar ta kuma bukaci gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da ya aika da jerin sunayen waɗanda ya zaɓa a matsayin kwamishinoni domin tantancewa da amincewa.

Kara karanta wannan

ADC ta fadi gwamnan da doka ta yarje wa Tinubu ya sauke daga kujerarsa

Mambobin Majalisar sun cimma wannan matsaya ne a zaman su na farko bayan karewar dokar ta bacin watanni shida da Tinubu ya sanya a Ribas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262