'Ban Manta ba,' Wike Ya Tuno Babbar Cin Amana da Aminu Tambuwal Ya Yi Masa a 2022
- Nyesom Wike ya zargi Aminu Tambuwal da zama dan siyasa mara alkibla, inda ya ce yana ta yawo tsakanin PDP, APC da ADC
- Ministan Abuja ya ce Tambuwal ya ci amanarsa a zaben fitar da gwani na PDP a 2022, lokacin da ya janye wa Atiku Abubakar
- Wike ya kuma caccaki Omoyele Sowore bisa kiran Shugaba Bola Tinubu da “dan ta'adda”, inda ya fadi babbar sa'ar da ya yi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, bisa zargin cewa bai cancanci a ba shi amanar shugabancin siyasa ba.
Wike ya bayyana Tambuwal a matsayin 'maci amana' wanda ba shi da alkibla a siyasa, inda ya ce, “Tambuwal ya kasance mutum mai yawan sauya ra'ayi saboda son zuciya.”

Source: Facebook
Ministan na babban birnin tarayya, ya yi wannan furuci ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Siyasa a yau' na Channels TV.
“Tambuwal ba shi alkibla” – Wike
Nyesom Wike ya ce:
“Mene ne Tambuwal ya sani game da shugabanci? A shekarar 1999, Tambuwal ya zama mataimaki na musamman ga Sanata Abdullah Wali. Daga nan ya juya masa baya, ya koma APP ko DPP, daga bisani ya dawo PDP. Ya zama kakakin majalisar wakilai.
“Bayan haka ya bar PDP ya koma APC. A 2017 ya koma PDP saboda burin yin takarar shugaban ƙasa. Yanzu kuma yana kokarin komawa ADC. Dubi irin salon siyasarsa, na rashin alkibla.
"A dalilinsa ne na kwaso taron gangamin PDP na kasa zuwa Fatakwal. Ta ya aka yi ma ya zama gwamna? Aliyu Wamakko ne ya kawo shi. A wa’adinsa na biyu a 2019 ma da kyar ya ci zaben da tazarar ƙuri’un da ba su kai 350 ba, a matsayinsa na gwamna mai ci.”
Legit Hausa ta fahimci cewa, Tambuwal ya lashe zaben gwamnan Sokoto da aka gudanar a ranar 9 ga Maris da karashen da aka yi a ranar 22 ga Maris, 2029, da kuri'u 512,002, yayin da Mista Aliyu, dan takarar APC ya samu kuri'u 511,660.
“Tambuwal ya ci amanata a zaben 2022” – Wike
Tsohon gwamnan Ribas ya ce ya rasa tikitin takarar shugaban ƙasa na PDP a 2022 saboda cin amanar da Tambuwal ya yi masa.
“Bukola Saraki bai janye wa Atiku ba, amma Tambuwal wanda kullum nake tsaya wa tsayin daka kan lamuransa, ya janye wa Atiku, kuma ya umarci wakilansa su zabi Atiku. Wannan shi ne tsantsar cin amana."
- Nyesom Wike.
Ya ƙara da cewa Tambuwal da Atiku sun dade suna sauya jam’iyya domin amfanin kansu, har ma Tambuwal yana fatan zama sanata idan Atiku ya lashe shugaban ƙasa.

Source: Facebook
Wike ya yi martani ga Sowore
Baya ga wannan, Wike ya kuma caccaki fitaccen ɗan gwagwarmayar siyasa, Omoyele Sowore, bisa kiran Shugaba Bola Tinubu “ɓarawo” a shafukan sada zumunta, inji rahoton Arise News.
Ya ce:
“Sowore ya yi sa’a saboda Shugaba Tinubu mutum ne da ke mutunta doka. Ko da mutum na adawa da shugaban ƙasa, ba zai yiwu a kira shi da sunan 'dan ta'adda' a fili ba.”
Ministan ya yi wannan furuci ne yayin ƙaddamar da hanyar Arterial Role N1 wadda ta haɗa Wuye District da Ring Road 2 a Abuja.
'Na yi magana da Fubara' - Wike
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan Abuja, Nyesom Wike ya tabbatar da cewa ya yi magana da Siminalayi Fubara kafin ya koma kan kujerar gwamna.
A ranar Laraba, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da janye dokar ta baci da ya sanya a jihar Rivers, lamarin da ya sa Fubara ya kamata ya koma aiki a ranar Alhamis.
Wike ya ce yanzu da Fubara ya dawo kan karagar mulki, za a hada kai domin yi wa jama'a aiki ba tare da rigingimun siyasa ba kamar yadda aka samu a baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


