Ministan Abuja Ya Kawo Cikas a PDP, Ya Dauko Batun Tsaida Jonathan Takara a 2027

Ministan Abuja Ya Kawo Cikas a PDP, Ya Dauko Batun Tsaida Jonathan Takara a 2027

  • Ministan Harkokin Abuja ya fito karara ya nuna adawarsa da shirin tsaida Goodluck Jonathan takarar shugaban kasa a 2027
  • Nyesom Wike ya bayyana cewa yana mamakin yadda mutanen da suka guje shi har ya fadi zabe a 2015, suke kokarin dawo da shi fagen siyasa
  • Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce yan siyasar da ke kokarin yaudarar tsohon shugaban kasar suna son tayar da rikici ne kawai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya soki waɗanda ke ƙoƙarin jawo tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya tsaya takara a 2027.

Mista Wike ya yi ikirarin cewa yan siyasa na kokarin dawo da Jonathan ne ba don komai ba sai son su haddasa rikici.

Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Hoton Ministan Harkokin Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Ministan Harkokin Abuja ya faɗi haka ne a daren Alhamis yayin da yake tsokaci7 kan lamarin a shirin Politics Today na Channels TV.

Kara karanta wannan

Wike ya tsallake rijiya, ya fadi yadda Janar na soja ya ba da umarnin harbe shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wadanne 'yan siyasa ke kokarin jawo Jonathan?

Dr. Jonathan ya shugabanci Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar PDP daga 2010 zuwa 2015 kafin ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari, ɗan takarar APC a wancan lokacin.

A watan Agusta, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa Jonathan na cikin jerin mutanen da PDP ke duba yiwuwar tsaidawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Baya ga Bala Mohammed, wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar sun nuna alamar cewa tsohon shugaban ƙasa na iya zama ɗan takarar PDP a zaben 2027.

Wike ya caccaki masu son dawo da Jonathan

Amma Wike, wanda shi ma ɗan PDP ne, ya ce abin takaici ne ganin waɗanda ke ƙoƙarin jawo Jonathan a yanzu, su ne suka hana shi nasarar wa’adi na biyu a 2015.

“Duk wanda yake cewa Jonathan ya dawo saboda zai yi wa’adi ɗaya kawai, to yana neman rikici ne kurum.
"Waɗannan su ne mutanen da suka guje shi a 2015. Me ya sa yanzu? Jonathan ya riga ya yi suna a duniya, amma suna son jawo shi cikin rikicin da bai kamata ba,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Ribas: Peter Obi ya zargi gwamnatin Najeriya da yi wa dimokuradiyya kisan mummuke

Jonathan da Wike.
Hoton tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da na Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @Good'uckJonathan, @govwike
Source: Twitter

'Akwai son zuciya a shirin dauko Jonathan a PDP'

Ministan Abuja ya ƙara da cewa dawo da Jonathan ko kuma wani ɗan takara daga Kudu bisa alkawarin “zai yi wa’adi ɗaya” wata dabara ce ta son zuciya, wadda ke barazana ga daidaiton siyasar Najeriya.

Jonathan, dai ya riga ya yi wa’adi ɗaya na shekaru huɗu, zai iya yin wa’adi ɗaya kacal idan ya sake zama shugaban ƙasa a 2027.

Kalaman Wike sun zo ne makonni bayan PDP ta yanke shawarar mika tikitin takarar shugaban ƙasarta zuwa yankin Kudu, in ji rahoton The Cable.

Ministan Abuja na fama da rashin lafiya?

A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya musanta jita-jitar cewa ya tafi kasashen waje domin neman magani, yana cewa siyasa kawai ake amfani da ita.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa lafiyarsa kalau, yana mai cewa masu yada wannan jita-jitar sai sun riga shi mutuwa.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi nazari, ya gano abin da yake tunanin ya hana kawar da 'yan bindiga a Najeriya

Ya kuma zargi masu yada wannan jita-jita da siyasa mara amfani, inda ya yi musu addu’ar rashin lafiya tare da tabbatar zai ci gaba da aiki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262