Abu Ya Girma: Abba Kabir Ya Kalubalanci Mulkin Ganduje, Ya Yi Masa Gorin Ayyuka
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kalubalanci tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana ayyukansa na alheri a Kano
- Abba Kabir ya kalubalanci tsohon shugaban APC ya kawo ayyuka hudu kacal da ya kammala a cikin shekaru takwas na mulkinsa
- Ya ce gwamnatin Ganduje ta zalunci malamai da ma’aikata, ta sayar da guraben aiki sannan ta wawure dukiyar jihar Kano ba tare da kunya ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Gwamna Abba Yusuf na Kano ya sake tabo tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje kan rashin katabus.
Abba Kabir ya caccaki tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, yana zarginsa da gazawa wajen kawo ci gaba da kuma karkatar da baitul malin jihar.

Source: Facebook
Abba Kabir ya dura kan Ganduje a Kano
A wajen raba guraben aiki ga malamai 4,315 a karkashin shirin BESDA, Yusuf ya kalubalanci Ganduje ya nuna ayyuka hudu kacal da ya kammala, cewar Daily Nigerian.
Ya ce gwamnatin Ganduje ta zalunci malamai da ma’aikata, ta sayar da guraben aiki sannan ta wawure dukiyar jihar ta hanyar barnatar da dukiya.
Ya ce:
"Sun lalata Kano, sun kwashe kudinku ba tare da gudanar da wani aiki mai muhimmanci ba, idan na fara tona musu asiri ba za ku iya iya yin barci ba.
"Sun kuntatawa malamai, ma'aikata da yan fansho, idan a lokacin mulkinsu ne da wannan damar duka sayar da ita za a yi gare ku.“

Source: Facebook
Abba ya fadi illar da Ganduje ya yi wa Kano
Gwamnan ya ce ya gaji baitul malin Kano babu kudi, inda asusun jihar ya nuna ragowar N9,075 kawai a lokacin mika mulki.
Duk da suka daga APC, Yusuf ya ce gwamnatinsa ta tsare biliyoyin Naira daga asara kuma tana karkatar da su zuwa manyan ayyukan cigaban jama’a.
“Shiyasa a yanzu kuke ganin daukar malamai aiki a gwamnati da hanyoyi da gyare-gyaren makarantu, inganta noma da tallafawa mata da matasa.
“Muna ci gaba da biyan yan fansho kudinsu, mun sake bude makarantun kwana, samar da wuta a tituna da sauran manyan ayyuka a Kano."
Kalubalen da Abba Kabir ya turawa Ganduje
Gwamna Abba Kabir har ila yau, ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin baya ta gudanar da mulki ba tare da yin muhimman ayyuka ba.
Ya kara da cewa:
"Idan za su iya, su nuna mana ayyuka guda hudu kacal da suka kammala a cikin shekaru takwas da suka yi suna mulki."
Ya umurci hukumar SUBEB da ta sake daukar karin malaman BESDA, domin ci gaba da inganta ilimi da samar da damar aiki ga matasa, The Guardian ta ruwaito wannan.
Yusuf ya kuma sanar da bayar da lamunin kudi N100,000 ga malamai 2,000 a karkashin hukumar domin tallafi da habaka rayuwa.
Kano ta yi fice a jarawabar NECO a Najeriya
Kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna farin cikinsa bisa yadda daliban Kano suka ci jarabawar kammala sakandire ta NECO a bana 2025.
A sakamakon jarabawar da hukumar NECO ta fitar, jihar Kano ta shiga gaba a jerin jihohin da suka samu sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan
Shehi ya soki zargin gina masana'antar fim, ya gargaɗi gwamna kan mummunar ƙarshe
Gwamnatin Kano ta ce wannan nasara alama ce da ke nuna cewa matakan da Gwamna Abba ke dauka suna kan hanya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

