Ibas: Mutumin Tinubu Ya Fara Fuskantar Matsala bayan Cire Dokar Ta Baci a Jihar Ribas
- Majalisar Dokokin jihar Ribas ta amince za ta gudanar da bincike kan yadda aka tafiyar da gwamnatin riko karkashin jagorancin Ibok-Ete Ibas
- Wannan mataki na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kawo karshen dokar ta-bacin da ya sanya a jihar Ribas
- A zaman farko bayan komawa aiki yau Alhamis, Majalisar ta kudiri aniyar gano yadda aka kashe kudin Ribas a mulkin riko na watanni shida
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Majalisar dokokin Ribas ta yanke shawarar gudanar da bincike kan yadda aka yi amfani da kuɗaden jihar a lokacin dokar ta-bacin watanni shiga.
Idan baku mana ba, Ibok-Ete Ibas ya yi mulki na tsawon watanni shida a matsayin shugaban riko na jihar Ribas bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta tattaro cewa bayan cire dokar a jiya, Majalisar Dokokin jihar Ribas ta koma aiki a yau Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar Dokokin Ribas ta koma aiki
A zaman farko da Majalisar ta gudanar, ta cimma matsayar gudanar da bincike kan yadda shugaban riko ya tafiyar da dukiyar jihar Ribas a tsawon watanni shida.
Haka kuma, majalisar ta bukaci gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, da ya aika da jerin sunayen waɗanda ya zaɓa a matsayin kwamishinoni domin tantancewa da amincewa.
Tun a jiya, watau 17 ga Satumba, 2025 ne shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya janye dokar ta baci, wanda hakan ya dawo da dukkan tsarin dimokuraɗiyya a jihar Ribas.
Kakakin majalisar, Martins Amaewhule, ne ya jagoranci zaman a ɗakin taro da ke cikin harabar majalisar, wadda har yanzu ake kan aikin gina ta.
Hakan dai ya faru ne sakamakon rusa tsohuwar majalisar da gwamnatin jihar Ribas karkashin Gwamna Fubara ta yi a baya lokacin rikicin siyasa.
Abin da ya jawo dokar ta-baci a Ribas
A ranar 18 ga Maris, Tinubu ya ayyana dokar ta baci a jihar Ribas saboda rikicin siyasa mai tsawo da ya samo asali daga sabani tsakanin gwamna Fubara da tsohon gwamnan, wanda yanzu shi ne Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Bayan haka, shugaban ƙasa ya dakatar da Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, da kuma ’yan majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Source: Facebook
A wannan lokaci ne ya nada Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) a matsayin shugaban rikon kwarya na jihar Fibas.
Majalisar Fibas ta ce za ta binciki yadda shugaban rikon ya yi amfani da dukiyar jihar a tsawon watanni shidada ya yi yana jagoranci, in ji rahoton The Nation.
Masoyan Fubara sun fito tarbarsa a Fatakwal
A wani rahoton, kun ji cewa magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun mamaye kofar Fadar Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbarsa bayan cire dokar ta-baci.
Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan gwamnan sun fito daga sassa daban-daban na kananan hukumomi 23 na jihar Ribas domin yi masa maraba a Fatakwal.
Sai dai har kawo yanzu ba a tabbatar da lokacin isowar gwamnan ba, haka kuma ba a san ko zai tsaya a kofar wajen ya yi magana da su ba kafin ya shiga ofis.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

