Gwamna Fubara na Shirin Komawa Mulki, Dandazon Mutane Sun Mamaye Gidan Gwamnati
- Magoya bayan Gwamna Siminalayi Fubara sun yi cincirindo a kofar gidan gwamnatin Ribas da ke birnin Fatakwal yau Alhamis
- Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan ke shirin komawa kan kujerarsa bayan watanni shida na dokar ta-bacin da aka sanya
- A jiya Talata ne shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo karshen dokar ta-bacin da ya sanya a jihar Ribas
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun mamaye kofar Fadar Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbarsa.
Cikin magoya bayan gwamnan akwai manyan jiga-jigai da tsofaffin mambobi na tsohuwar kungiyar Simplified Movement, wacce aka rushe ta daga baya.

Source: Facebook
The Nation ta tattaro cewa daga cikinsu akwai tsohon Kakakin majalisar dokokin mutum uku da aka rusa, Victor Oko-Jumbo, wanda ya jagoranci wasu wajen jiran gwamnan.
Magoya bayan Fubara sun fito tarbarsa
Rahotanni sun nuna cewa magoya bayan gwamnan sun fito daga sassa daban-daban na kananan hukumomi 23 na jihar Ribas domin tarbar dawowarsa a Fatakwal.
Wani daga cikinsu ya bayyana cewa sun zo ne su tarbi mai girma gwamna yayin da zai koma kan mulki, wanda dama hakkinsa ne.
Legit Hausa ta tattaro cewa daruruwan masoya da masu fatan alheri na ci gaba da tururuwar zuwa kofar shiga gidan gwamnatin Ribas da ke Fatakwal da safiyar yau Alhamis.
Yaushe gwamnan zai isa gidan gwamnati?
Sai dai har kawo yanzu ba a tabbatar da lokacin isowar gwamnan ba, haka kuma ba a san ko zai tsaya a kofar wajen ya yi magana da su ba kafin ya shiga ofis.
An ga mata sanye da kayan ado masu launi-launi, kungiyoyin raye-raye, matasa da wasu dattawa a cikin yanayi na murna yayin da suke jiran zuwansa.
Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya cire dokar ta-bacin da ya sanya a jihar Ribas watanni shidada da suka gabata.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya dage dokar ta-bacin Ribas
Shugaba Tinubu ya sanar da cewa dokar za ta kare a karshen ranar Talata, sannan ya umarci Gwamna Fubara da Yan Majalisar Dokokin Ribas su koma aiki yau Alhamis.
Cire dokar ta bacin ya ja hankalin masu ruwa da tsaki da manyan jiga-jigai a kasar nan, inda wasu ke nuna farin cikinsu da ci gaban da aka samu a jihar Ribas, wasu kuma na suka.
A halin yanzu dai magoya bayan Fubara sun kewaye gidan gwammati da ke Fatakwal, suna dakon isowar mai girma gwamna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Dalilin Tinubu na dage dokar ta-bacin Ribas
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ya janye dokar ta baci ne bayan bayanan sirri sun nuna al'amura sun daidaita tsakanin jagororin Ribas.
Ya ce duba da wannan ci gaba da aka samu, babu dalilin da zai sa dokar ta ci gaba da zama bayan lokacin da aka dibar mata ya kare.

Kara karanta wannan
Sardauna: Gwamna ya karrama Ahmadu Bello, ya yi alƙawarin ci gaba da yaɗa manufofinsa
Tinubu ya yi kira ga gwamnoni da ‘yan majalisa a fadin kasar nan da su tuna cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne ginshikai na kawo wa ‘yan Najeriya amfanin dimokuraɗiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

