A Karshe, Shugaba Tinubu Ya Cire Dokar Ta Bacin da Ya Sanya a Jihar Ribas

A Karshe, Shugaba Tinubu Ya Cire Dokar Ta Bacin da Ya Sanya a Jihar Ribas

  • Gwamna Siminalayi Fubara da yan Majalisar Dokokin jihar Ribas za su koma bakin aiki gobe Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025
  • Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya sanar da hakan bayan cire dokat ta bacin watanni shida da ya sanya tun a watan Maris
  • Tinubu ya bayyana cewa ya gamsu da yadda al'amura suka daidaita a jihar Ribas, don haka babu dalilin da dojar za ta ci gaba da zama

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya cire dokar ta-bacin watanni shida da ya sanya a jihar Ribas tun ranar 18 ga watan Maris, 2025.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa dokar ta-bacin za ta ƙare da tsakar dare yau Laraba, 17 ga watan Satumba, 2025.

Shugaba Tinubu tare da Gwamna Fubara da Wike.
Hoton Shugaba Tinubu tare da Gwanna Fubara da Wike a fadar shugaban kasa Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai girma shugaban kasa ya rattaba wa hannu da kansa kuma aka wallafa ta a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Rivers: Ƴan majalisa sun dauki matakin farko bayan Tinubu ya janye dokar ta baci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya dage dokar ta-bacin Ribas

A sanarwar, Tinubu ya ce ya gamsu da ci gaban da jihar Ribas ta samu a lokacin dokar ta-bacin.

Shugaba Tinubu ya ce:

“A yau ina farin cikin cewa, daga bayanan sirrin da na samu, akwai sabon yanayi na fahimtar juna, shiri mai ƙarfi da kuma ƙwazo daga dukkan ɓangarorin da abin ya shafa a Jihar Ribas.
"Wannan ci gaba ne mai matuƙar daɗi a gare ni kuma babbar nasara ce a gare mu. Saboda haka ban ga wani dalilin da zai sa dokar ta-baci ta ci gaba da wanzuwa ba bayan watanni shida da na sanar tun farko.”

Tinubu ya maida Fubara da yan Majalisa

Tinubu ya kuma umarci Gwamna Siminalayi Fubara da Majalisar Dokokin Jihar Ribas karkashin jagorancin Rt. Hon. Martins Amaewhule su koma bakin aiki gobe Alhamis.

“Don haka, ina farin cikin sanar da cewa dokar ta-baci a Jihar Rivers za ta ƙare daga tsakar daren yau.

Kara karanta wannan

Manyan 'yan siyasa 4 da za su koma bakin aiki bayan janye dokar ta baci a Rivers

"Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, Ngozi Nma Odu, tare da ’yan majalisar dokoki na jihar da Kakakinsu, Martins Amaewhule, za su koma bakin aiki daga ranar 18 ga Satumba, 2025.”

- Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Hoton mai girma shigaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ofis Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya ja hankalin gwamnoni

Tinubu ya kuma yi kira ga sauran gwamnonin jihohi da majalisun dokoki su fahimci cewa babu yadda za a iya samar da ribar dimokuraɗiyya sai cikin yanayi na zaman lafiya da tsari.

“Ina roƙonku da ku dauki wannan fahimta ta kasance abin da zai jagoranci ayyukanku a kowane lokaci," in ji shi.

APC ta nemi Gwamna Fubara ya dawo jam'iyyar

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas ta fara shirin jawo ra'ayin Gwamna Siminalayi Fubara ya sauya sheka kafin bikin dawo da shi kan mulki.

Mai magana da yawun APC na Ribas, Darlington Nwauju, ya bayyana cewa jam'iyyar a shirye take ta karbi Gwamna Fubara cikin farin ciki.

Nawauju ya tabatar wa Fubara cewa a bisa tsarin APC, da zarar ya amince da sauya sheka, shi ne zai zama jagoran jam'iyyar a jihar Ribas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262