Shirin Sauya Gwamnatin Tinubu, PDP Ta Fadi Matsayarta kan Takarar Jonathan a 2027

Shirin Sauya Gwamnatin Tinubu, PDP Ta Fadi Matsayarta kan Takarar Jonathan a 2027

  • Jam'iyyar PDP a jihar Abia ta ce tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na da damar yin takarar shugabancin ƙasa a 2027
  • Amma shugaban PDP na jihar, Elder Abraham Amah ya ce, dole Jonathan ya bi ƙa'idojin jam'iyyar idan yana son tikitin takarar
  • Elder Amah ya ce har yanzu Jonathan bai gabatar mata da kudurinsa na son tsayawa takara ba, amma kofarta a bude take

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia – Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, na da cikakken 'yancin neman takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Sai dai kuma, jam'iyyar reshen jihar Abia, ta ce ya zama dole Goodluck Jonathan ya bi dukkan matakan da dokar jam’iyya ta shimfida don neman takarar.

Jam'iyyar PDP ta ce kofarta a bude take ga Jonathan idan yana son yin takarar shugaban kasa a 2027.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zaune a dakin taron da PDP ta shirya a Abuja. Hoto: @GEJonathan
Source: Facebook

'Jonathan na da hakkin tsayawa takara' - PDP

Kara karanta wannan

"An yi watsi da ni," Dan Majalisa ya tattara kayansa ya fice daga jam'iyyar APC

Shugaban PDP na jihar Abia, Elder Abraham Amah, ya bayyana haka ne a yayin hira da wakilin jaridar The Punch, a Umuahia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, hankalin jam’iyyar ya kai ga jita-jita kan ko Jonathan ya cancanci ya samu tikitin takarar kujerar shugaban kasa a karkashin PDP.

Elder Abraham ya ce:

"Kwarai ya cancanci ya tsaya takara, yana da hakkin yin hakan. Amma dai ba za a yi son rai wajen ba wani tikiti ba, dole za a fitar da dan takara ne ta hanyar sahihin zaben fitar da gwani."

Kofar PDP a bude take ga 'yan takara

Elder Amah ya ce PDP jam’iyya ce da take bude kofarta ga kowa da kowa, kuma duk wani dan jam’iyya da yake ganin ya cancanta, to zai samu damar tsayawa takara.

Ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, a matsayinsa na jagora kuma mutu mai kima a PDP, na da damar neman tikitin shugaban kasa a jam'iyyar.

Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ci gaba da tabbatar da dimokuradiyya, adalci da daidaito ga duk wadand za su tsaya takara a karkashinta.

Kara karanta wannan

"Babu ADC": Jigon PDP ya hango yadda za ta kaya a zaben 2027

Makomar Jonathan na hannun wakilan PDP

Shugaban jam’iyyar ya ce akwai kungiyoyi masu tasiri a PDP da ke ganin Jonathan ne ya dace ya samu tikitin jam’iyyar domin kara wa da Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Sai dai Elder Amah ya ce, wakilan wakilan jam’iyyar da za su kada kuri’a a taron zaben fitar da gwamni na shugaban kasa ne za su yanke makomar Jonathan.

Ya kuma ce PDP reshen jihar Abia za ta ci gaba da bude kofa ga kowanne dan siyasa har sai lokacin da wakilai za su zabi wanda zai zama dan takarar jam’iyyar.

Jam’iyyar na jiran matsayar Jonathan

Amah ya ce PDP Abia tana bibiyar dukkan ci gaban siyasa a kasa da cikin jam’iyya kafin ta fito da matsaya a hukumance.

Ya ce yanzu haka Jonathan bai gabatar da manufofi ko budurinsa na shiga zaben 2027 ga jam'iyyar, reshen Abia ba, amma kofofinsu a bude suke a gare shi.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

“Mun jajirce wajen tabbatar da gaskiya, adalci da dimokuradiyya yayin da muke shirin gudanar da babban zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa."

- Elder Abraham Amah.

Jam'iyyar PDP ta ce har yanzu Jonathan bai gabatar mata da kudurinsa na son tsaya wa takara a 2027 ba.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan yana jawabi a taron da aka shirya kan zabukan dimokuradiyya a Yammacin Afrika. Hoto: @GEJonathan
Source: Twitter

Doka ta ba Jonathan damar sake tsaya wa takara

Tun da fari, mun ruwaito cewa, ana ta hasashen wadanda za su tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2027 mai zuwa, inda ake yawan ambaton Goodluck Ebele Jonathan.

Sai dai, mutane na tababa kan ko Jonathan na da hurumin sake zaman shugaban Najeriya bisa kundin tsarin mulki? La'akari da cewa an rantsar da shi sau biyu a baya.

Bisa kundin tsarin mulki, hukuncin kotu, da ra’ayoyin masana, Goodluck Jonathan na da cikakkiyar damar tsaya wa takara a zaben 2027, kamar yadda binciken Legit Hausa ya nuna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com