"Za Mu Yi Farin Ciki," APC Ta Ja Hankalin Gwamna, Ta Nemi Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

"Za Mu Yi Farin Ciki," APC Ta Ja Hankalin Gwamna, Ta Nemi Ya Fice daga Jam'iyyar PDP

  • APC ta kara yin kira ga gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen dawo da Fubara kan mulki bayan watanni shida na dokar ta baci
  • Mai magana da yawun APC reshen jihar Ribas, Darlington Nwauju, ya ce kamata ya yi Fubara ya shiga APC kafin ranar dawo da shi kan mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Rivers - Jam’iyyar APC reshen Jihar Ribas ta fara shirin jawo ra'ayin Gwamna Siminalayi Fubara ya sauya sheka kafin bikin dawo da shi kan mulki.

Mai magana da yawun APC na Ribas, Darlington Nwauju, ya bayyana cewa jam'iyyar a shirye take ta karbi Gwamna Fubara cikin farin ciki da murna.

Gwamna Siminalayi Fubara.
Hoton Gwamna Fubara na jihar Ribas Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Source: Instagram

Nwauju ya yi wannan furuci ne a cikin shirin The Morning Brief na tashar Channels TV a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya yi magana kan komawa ADC bayan rashin samun mafaka a APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta ci gaba da kokarin jawo Fubara

“Da ni ne Gwamnan Jihar Ribas, da zarar na dawo kan mulki a ranar Alhamis, zan sanar da cewa na koma APC.
"Ina ganin ya kamata gwamna ya shiga APC, kuma da farin ciki za mu karɓe shi cikin jam’iyyarmu.”

Da aka tambaye shi ko Fubara zai zama jagoran APC na Ribas idan ya shiga jam’iyyar, Nwauju ya amsa da cewa hakan tabbas ne.

Gwamna Fubara zai karbi jagoranci a Ribas

Ya ce bisa tsarin jam’iyyar, duk wani gwamna da ya shiga APC kai tsaye shi ne jagoran jam’iyyar a jiharsa.

"Da zarar ya amince ya shigo APC, ya zama jagoran jam’iyyar a jihar,” in ji Nwauju.

Har ila yau, ya yi tsokaci kan mulkin Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (mai ritaya) wanda ya shugabanci jihar a matsayin shugaban riko na tsawon watanni shida.

APC ta nemi a binciki gwamnatin riko?

Kara karanta wannan

2027: APC, PDP sun fara nuna wa juna yatsa kan karya dokar INEC

Nwauju ya kuma jaddada cewa babu inda jam'iyyar APC ta nemi a gudanar da bincike kan mulkin da shugaban Ribas na rikon kwarya ya yi, in ji rahoton Punch.

"Babu lokacin da APC ta aika takardar neman a binciki Ibas kan yadda ya gudanar da mulki a cikin watanni shida da suka wuce.
"Kasafin kuɗin da ya yi amfani da shi ya fito ne daga Majalisar Tarayya. Akwai kwamitin Majalisar Wakilai da ke duba lokacin dokar ta baci.
"Ina sa ran wannan kwamitin zai gudanar da bincike sosai, ya kuma sanar da ’yan Najeriya abin da suka gano, domin hakan na daga cikin ayyukan su na doka,” in ji shi.
Jam'iyyar APC.
Tutar jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma gwamna da aka dakatar, Siminalayi Fubara, za su dawo Najeriya a ranar Talata, kafin bikin dawo da gwamnan kan mulki.

Tinubu da Fubara na shirin dawowa Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Siminalayi Fubarai da aka dakatar za su dawo Najeriya a yau Talata.

Matakin ya zo a daidai lokacin da ake shirin kammala mulkin rikon kwarya da Shugaba Tinubu ya kakaba wa jihar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"An yi watsi da ni," Dan Majalisa ya tattara kayansa ya fice daga jam'iyyar APC

Yanzu haka, hankula sun karkata kan shirin mika mulki wanda zai kawo ƙarshen mulkin rikon kwarya na wucin gadi da Tinubu ya sa a jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262