Sheikh Isa Pantami Ya Gana da Peter Obi, Ya Jero Abubuwan da Suka Tattauna

Sheikh Isa Pantami Ya Gana da Peter Obi, Ya Jero Abubuwan da Suka Tattauna

  • Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Pantami ya karbi bakuncin Mista Peter Obi a gidansa da ke Abuja
  • Pantami ya ce ya tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasa da tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP, Mista Obi
  • Daga cikin bangaororin da suka tattauna a cewar Pantami akwai noma, tattalin arziki, fasahar AI da hadin kan al'umma mabanbanta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar LP, Mista Peter Obi ya ziyarci Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami a babban birnin tarayya Abuja.

Pantami, Tsohon Ministan Sadarwa a Najeriya ya ce ya gana da Peter Obi kuma sun tattauna muhimman batutuwa da suka shafi kasa.

Peter Obi ya ziyarci Pantami.
Hoton Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami tare da Peter Obi Hoto: @ProfIsaPantami
Source: Twitter

Peter Obi ya je wajen Isa Pantami

Farfesa Isa Pantami ya wallafa bidiyonsa tare da Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra, a shafinsa na Facebook yau Talata, 16 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta hakura da lafta sabon harajin shigo da layayyaki Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan siyasa da jam'iyyu ke shirye-shiryen tunkarar babban zaben 2027.

Pantami na daya cikin wadanda ake kiraye-kirayen su fito takara a zaben 2027, inda al'ummar jihar Gombe ke son tsohon ministan ya nemi kujerar gwamna.

A gefe guda kuma Peter Obi na daya daga cikin manyan jagororin adawa da suka yi hadaka da nufin kalubalantar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben da ke tafe.

Obi ya yi takara a zaben shugaban kasar 2023 amma bai samu nasara ba kuma ana kyautata zaton zai sake neman takara a zabe na gaba.

Abin da Pantami da Obi suka tattauna

Da yake karin haske kan ganawarsa da Peter Obi, Farfesa Pantami ya ce sun tattauna muhimman batutuwa ciki har da fannonin noma, tattalin arziki da fasahar AI.

“A daren jiya, na karɓi bakuncin tsohon Gwamnan Jihar Anambra, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 na jam’iyyar LP, Mista Peter Obi.

Kara karanta wannan

Tinubu, Fubara sun dawo Najeriya ana shirin dawo da gwamnan Ribas kujerarsa

"Mun tattauna kan fannoni daban-daban ciki har da noma, tattalin arziki, ilimi, fasahar zamani watau AI, kididdiga halin da ake ciki a duniya, da kuma haɗin kai a cikin bambance-bambancen da muke da shi.

- In ji Sheikh Isa Pantami.

Farfesa Isa Ali Pantami.
Hoton Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Pantami Hoto: Prof. Isa Pantami
Source: Facebook

Sheikh Pantami ya yaba da ziyarar Peter Obi

Tsohon Ministan, wanda ya yi aiki a gwamnatin Marigayi Muhammadu Buhari, ya ƙara da cewa shi da iyalinsa sun yi matuƙar farin ciki da wannan ziyara.

“Ni da iyalina mun yaba ƙwarai da wannan ziyara,” in ji shi.

Peter Obi ya ziyarci Obasanjo da Oba Ladoja

A wani labarin, kun ji cewa jagoran LP na kasa, Peter Obi ya kai ziyara ta musamman ga tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo da Sarkin Ibadan mai jiran gado.

Da yake magana bayan ganawar, Obi ya yi kira ga daukacin jama'a da su rungumi haɗin kai da zaman lafiya, inda ya ce babu wata ƙasa da za su iya kira tasu sai Najeriya.

Ya ƙara da cewa, a duka ziyarorin biyu, sun tattauna kan yanayin ƙasar da kuma yadda za a samar da haɗin kai, soyayya, adalci, da ci gaban jama'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262