'Umarni Na Bi,' Akawun Majalisa Ya Tsame Kansa daga Hana Sanata Natasha Dawo wa Ofis
- Ofishin Akawun Majalisar Dattawa ya bayyana cewa har yanzu ba a sahalewa Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta dawo aiki ba
- Sai dai jami'in ya wanke kansa daga batun, inda ya ce aikinsa na gudanarwar majalisa ne kawai ba yanke hukunci ko saba shi ba
- Sanata Natasha da wakiltar Kogi ta Tsakiya da majalisa ta dakatar watanni shida da su ka wuce ta nemi dawo wa aiki, amma ofishin ya hana
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Ofishin Akawun Majalisar Dattawa ya bayyana cewa ba shi da ikon dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan zauren majalisa.
Har yanzu ana tataburza tsakanin Sanata Natasha mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar watanni shida da su ka gabata, kuma majalisar ta murza gashin baki, inda ta hana ta dawo wa.

Source: Facebook
Arise News ta wallafa cewa sai dai Ofishin Akawun da ke fitar da sanarwar cewa Sanata Natasha ta ci gaba da zaman gida, ya bayyana cewa ba shi da hurumin yanke hukunci dawo da ita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akawun Majalisa ya magantu kan Natasha
Jaridar Punch ta wallafa cewa cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na ofishin, Mullah Bi-Allah, ya fitar a ranar Litinin a birnin Abuja, ya bayyana aikin ofishin.
Ya bayyana cewa aikin ofishin bai wuce na gudanarwar majalisa ba, saboda haka ba shi da hurumin duba ko janye kudurin da Majalisar Dattawa ta zartar.
A cewarsa:
“Akawun majalisa ba shi da ikon duba, janye ko fassara shawarar da Majalisar Dattawa ta yanke.”
Majalisa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan, a ranar 6 ga Maris, 2025, bayan dambarwarta da Shugaban Majalisa, Godswill Akpabio, wanda daga baya ta zargi da cin zarafinta.
A ranar 4 ga Satumba, Sanata Natasha ta rubuta takarda zuwa Ofishin Akawun Majalisar Tarayya domin sanar da shirin ta na dawowa bakin aiki.

Kara karanta wannan
Natasha: NLC ta fara shirin hada gangamin zanga zanga kan hana Sanata koma wa majalisa
Sai da ofishin ya ce:
“Wannan ofishi ya isar da wasiƙar zuwa ga shugabancin Majalisar Dattawa, wanda suka bayyana cewa batun yana gaban kotun daukaka kara, don haka duk wani sauyi sai dai idan majalisa ta sake zartar da sabuwar doka ko kuma kotu ta yanke hukunci kai tsaye.”
Bi-Allah ya ce sun samu wasikar koke daga lauyoyin Sanata Natasha, M. J. Numa & Partners LLP, inda suka zargi ofishin da wuce gona da iri tare da barazanar daukar matakin doka.

Source: Facebook
Amma ya ce:
“Dole ne a fahimta cewa yanke hukuncin ko Natasha za ta iya dawowa majalisa bayan wa’adin dakatarwarta ba aikin ofishinmu ba ne, sai dai Majalisar Dattawa da kuma kotu.”
NLC za ta yi zanga-zanga saboda Natasha
A baya, mun wallafa cewa Shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), Comrade Joe Ajaero, ya kalubalanci Majalisar Dattawa ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio.
Ya ce matakin da majalisa ta dauka kan hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya komawa bakin aikinta, duk da cikar wa’adin dakatarwar ya saba doka.
Ajaero ya yi gargaɗi cewa idan Majalisar Dattawa ba ta yi abin da ya dace ba, ƙungiyar NLC za ta fitar da dubunnan ‘ya’yanta domin nuna adawa da ci gaba da tauye hakkin Natasha.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

