Kalaman Atiku Sun Yi Zafi, APC Ta Dauko Tarihi har da Lokacin Marigayi 'Yar'adua

Kalaman Atiku Sun Yi Zafi, APC Ta Dauko Tarihi har da Lokacin Marigayi 'Yar'adua

  • Kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kan yunwa da talauci ba su yi wa jam'iyyar APC dadi ba
  • Atiku dai ya yi ikirarin cewa babu wata alama da ke nuna Tinubu zai iya magance yunwa da talauci a shekaru biyu da ya yi a kan mulki
  • Mai magana da yawun APC, Felix Morka ya ce yan Najeriya sun san waye Atiku, ba za su zabe shi ya zama shugaban kasa a 2027 ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta ce ‘yan Najeriya ba sa tunanin zabar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaki Atiku Abubakar, a zaben 2027.

APC ta yi ikirarin cewa Atiku ya samu dama a baya amma ya gaza, don haka babu dalilin da 'yan Najeriya za su zabe shi ya zama shugaban kasa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Buba Galadima: Na kusa da Kwankwaso ya fallasa makarkashiyar Tinubu kan 'yan adawa

Felix Morka.
Hoton Mai Magana da Yawun Jam'iyyar APC na Kasa, Felix Morka Hoto: @officialAPCNig
Source: Facebook

Mai magana da yawun APC, Felix Morka, ne ya bayyana haka ranar Litinin a shirin siyasa na tashar Channels TV mai suna Politics Today.

APC ta tunawa 'yan Najeriya tarihin Atiku

Ya ce idan har Atiku ya yi shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa ba tare da inganta rayuwar ‘yan Najeriya ba, babu abin da zai iya yi yanzu.

“A lokacin mulkinsu, ba su kawar da talauci ba, ba su magance yunwa ba, ba su kawo karshen rashin tsaro ba, ba su kawo karshen abubuwan da suka jefa ‘yan Najeriya a cikin kunci ba.
"Sannan suka mika mulki ga wata gwamnati da ta yi shekaru takwas, ita ma ba ta kawar da talauci ba. Saboda haka abin takaici ne mutane su zauna suna fadin irin wadannan kalamai."

- Felix Morka.

Abin da ya sa APC ta dauko tarihin mulkin PDP

Morka ya dauko wannan tarihi na mulkin PDP ne yayin da yake mayar da martani kan sukar da Atiku ya yiwa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku ya sake yi wa gwamnatin Tinubu saukale, ya fadi abin da ta gaza magancewa

Atiku ya ce shekara biyu da fara mulkin Shugaba Bola Tinubu, har yanzu babu wata alama da ke nuna cewa zai iya shawo kan yunwa da talauci da ke addabar kasa.

"Yan Najeriya ba za su zabi Atiku ba" - APC

Kakakin APC ya ci gaba da martani da cewa:

“Ba zan tsaya ina bata lokaci kan maganar Atiku ba. Na yi imani ‘yan Najeriya suna kallon abin da ke faruwa.
"Ba na tunanin yan Najeriya suna damuwa da abin da yake fada domin sun san dalilin da yasa yake fadar hakan shi neman mulki kawai yake yi.
"Yana tunanin idan ya rika zagin gwamnati da fadin karya, ‘yan Najeriya za su zabe shi. Amma sau da dama ‘yan Najeriya sun ki shi. Kuma gaskiya, ba na ganin za su zabi Atiku."
Shugaban APC, Nentawe da Atiku Abubakar.
Hoton shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe da Alhaji Atiku Abubakar Hoto: @OfficialAPCNig, @Atiku
Source: Twitter

Morka ya kuma kare manufofin Shugaba Tinubu, yana mai cewa duk da cewa sun kawo wahala a farko, yanzu an fara ganin sakamako kuma Najeriya ta fara dawo wa kan turba, in ji Leadership.

Fadar shugaban kasa ta soki Atiku

A wani labarin, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta tanka wa Atiku Abubakar bayan ya zargi Bola Tinubu da gaza magance yunwa da talauci.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Atiku ya raba gardama kan shirin ficewa daga PDP zuwa APC

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa ikirarin da Atiku ya yi dangane da halin da ake ciki a Najeriya ba gaskiya ba ne.

Ya ce a shekaru biyu da watanni biyar kacal a kan karagar mulki, Najeriya na ganin sauye-sauyen da su ka tabbatar da nagartar shugabancin Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262