Ana Batun Zaben 2027, Majalisar Dinkin Duniya Ta Aiko Sako ga Jam'iyyu da 'Yan Siyasar Najeriya

Ana Batun Zaben 2027, Majalisar Dinkin Duniya Ta Aiko Sako ga Jam'iyyu da 'Yan Siyasar Najeriya

  • Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta gargadi APC, PDP, ADC da sauran jam'iyyun siyasa game da cin mutuncin juna gabanin zaben 2027
  • Walilin majalisar a Najeriya, Mohamed Malick Fallya ja hankalin yan siyasa su gujewa amfani da kalaman kiyayya da bata juna
  • Shugaban Hukumar Zabe (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu ya nuna damuwa kan yadda kalaman kiyayya ke karuwa a siyasar Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar Dinkin Duniya (UN) ta gargadi duka jam’iyyun siyasa da shugabanninsu a Najeriya da su guji yin amfani da kalaman kiyayya yayin da ake shirye-shiryen zaben 2027.

Wannan gargadin ya fito ne daga wakilin UN a Najeriya kuma mai kula da ayyukan jin ƙai, Mista Mohamed Malick Fall.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Mohamed Malick Fall.
Hoton Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya kuma shugaban harkokin jin kai, Mohamed Malick Fall Hoto: @NhrcNigeria
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa Mohamed ya yi wannan gargadi ne a wani taro da Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa (NHRC) tare da Majalisar Dinkin Duniya suka shirya a Abuja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan hadaka na shirin sauya jam'iyya daga ADC zuwa ADA,? An ji yadda lamarin yake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni dai yan siyasa suka fara shirye-shiryen yadda za su samu mulki a zabe mai zuwa, wanda hakan ya jawo rikice-rikice da musayar kalaman batanci, kiyayya da zage-zagen siyasa.

Sakon Majalisar Dinkin Duniya ga jam'iyyu

Da yake jawabi ga wakilan jam’iyyun siyasa da sauran masu ruwa da tsaki, Mohamed Malick Fall ya jaddada cewa demokradiyya ta ƙunshi haɗin kai, ra’ayoyi, da mutunta juna cikin girmamawa.

Ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da su zama abin koyi ta hanyar mayar da hankalinsu kan manufofi da tsare-tsaren ci gaba a maimakon zagi ko kalaman da ka iya jawo rabuwar kai.

“A zamanin yanzu na kafafen sada zumunta, kalaman kiyayya suna yaduwa da sauri kuma suna isa ga mutane da yawa fiye da da. Wannan na iya barazana ga zaman lafiya, mutunci, da tsaron jama’a,” in ji shi.

Wakilin UN ya yi gargadin cewa ya zama dole a tabbatar da ingancin bayanai a lokacin zabe, inda ya bayyana hakan a matsayin adalci, daidaito da amincin a harkokin gudanar da zabe.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sha alwashin hana Tinubu samun tazarce a 2027? Gaskiya ta fito

Ya ce ƙarya da kalaman tayar da hankali na iya rusa amincewar jama’a da yaudarar masu kada kuri’a, in ji rahoton Guardian.

Ya shawarci jam’iyyun siyasa da su bi ƙa’idojin da ke hana cin mutuncin juna, su kuma rungumi tattaunawa cikin gaskiya da mutunta juna, tare da yin aiki tare da kafafen yada labarai domin dakile yada labaran ƙarya.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu.
Hoton Shugaban Hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmud Yakubu a wurin taron masu ruwa da tsaki a Abuja Hoto: @INECNigeria
Source: Twitter

Hukumar INEC ta yi alkawarin zaben adalci

A jawabinsa a wurin taron, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya nuna damuwa kan yadda cin mutunci da da bata juna ke ƙaruwa a harkokin siyasa.

Ya tabbatar da cewa hukumar INEC za ta samar da dama bisa adalci ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu a zabe mai zuwa.

Yakubu, wanda Lauya Sulaiman Ibrahim (SAN) ya wakilta, ya ce nasarar zabe ta dogara ne da yadda ‘yan siyasa da magoya bayansu za su nuna wa jama'a kansu.

INEC ta nuna damuwa kan fara kamfe yanzu

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Zabe (INEC) ta nuna damuwa matuka kan yadda 'yan siyasa da magoya bayansu ke kara tsunduma cikin kamfen tun yanzu.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Ministan Tinubu da gwamna a APC? An samu bayanai

INEC ta ce ba ta jin dadin yadda 'yan siyasa ke karya dokar zabe domin haramun ne a dokar Najeriya fara kamfe kafin lokacin da aka tanada.

Hukumar ta ce wadannan ayyuka na ‘yan siyasa na iya shafar zaman lafiya da adalci a lokacin zabe, tare da haddasa rudani a zukatan al’umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262