"Ka Daina Kawo Rudani": An Shawarci Wike Ya Zaba tsakanin Jam'iyyar APC, PDP

"Ka Daina Kawo Rudani": An Shawarci Wike Ya Zaba tsakanin Jam'iyyar APC, PDP

  • Tonye Cole ya bukaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fito fili ya bayyana jam’iyyar da yake ciki
  • Tsohon dan takarar gwamnan ya ce ya kamata Wike ya bar PDP ya koma APC domin kaucewa kawo rudani a siyasa
  • Wike dai ya sha fitowa sau da dama yana cewa har yanzu yana cikin PDP duk da yana aiki a gwamnatin tarayya karkashin APC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Rivers - Tsohon dan takarar gwamna a jihar Rivers karkashin jam’iyyar APC, Tonye Cole, ya ba ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, shawara.

Tonye Cole ya bukaci Nyesom Wike cewa ya fito fili ya bayyana jam'iyyar siyasar da yake ciki domin kawar da rudani.

Tonye Cole ya bukaci Wike ya koma APC
Hoton Ministan Abuja, Nyesom Wike da Tonye Cole Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Tonye Cole
Source: Facebook

Tonye Cole ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na Channels Tv a ranar Juma’a, 12 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

"Ta mutu": Sanata Dino Melaye ya fadi masu ikon juya jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara aka ba Nyesom Wike?

Ya ce ya kamata Wike ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC, domin karfafa dimokuradiyya da kuma ba sauran jam’iyyu damar samun ci gaba ba tare da shisshigi ba.

Tonye Cole ya bayyana cewa ya kamata Wike ya fice daga PDP zuwa APC don kawar da duk wani rudani kan inda ya sa gaba a siyasarsa.

A cewarsa, idan Wike ya bayyana inda ya dosa a siyarsa, yanayin siyasar jihar Rivers zai daidaita.

"Shin Wike na APC ne ko PDP? A halin yanzu dai, mun san PDP yake ciki. Ba za mu ci gaba da rikita masu kada kuri’a a Rivers da Najeriya baki daya ba, domin hakan hatsari ne ga dimokuradiyya."
"Mutumin da kawai ya rage ya bayyana inda yake a siyasarsa, shi ne Minista Nyesom Wike. Abin da zan roke shi shi ne ya zo cikin APC a matsayin mutumin kirki."

Kara karanta wannan

Ministan Abuja, Wike ya yi martani ga Tambuwal kan zargin cin amana

"Ya bar PDP, ya shiga APC domin mu tsaya a wuri daya, babu rabuwar kai, babu rudani.”

- Tonye Cole

Amfanin sauya shekar Nyesom Wike

Tonye Cole ya kara da cewa hakan zai bai wa sauran jam’iyyu kamar PDP, ADC, LP da YPP damar yin siyasa ba tare da shisshigi ba.

Tonye Cole ya ba Wike shawara ya bar PDP
Hoton tsohon dan takarar gwamnan Rivers, Tonye Cole Hoto: Tonye Cole
Source: UGC
"Dimokuradiyya dai tana nufin kowace jam’iyya ta samu damar gina karfinta sannan a hadu a fafata a siyasa. Idan haka ya tabbata, za mu san ainihin inda muke."

- Tonye Cole

Sai dai Wike, wanda ya taba zama gwamnan Rivers, ya sha nanata cewa yana nan a jam’iyyar PDP duk da cewa yana aiki a cikin gwamnatin tarayya karkashin APC.

Wike ya sanya tara kan filaye a Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya sanya tarar N5m ga manyan mutane a Abuja.

Nyesom Wike ya sanya tarar ne kan mutanen bisa zargin sauya amfani da filaye ba tare da neman sahalewar gwamnati ba.

Kara karanta wannan

'Sanatoci da 'yan Majalisar Wakilai da dama sun shiga jam'iyyar hadaka, ADC'

Matakin dai ya shafi filaye da gidajen manyan tsofaffin gwamnati da suka hada da alkalai, gwamnoni, hafsoshin soja da kuma hukumomin gwamnati da na masu zaman kansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng