Tun kafin 2027, Ana Ganin Yan Najeriya Sun Fi Ambatar Sunan 'Dan PDP Fiye da Tinubu
- 'Yan siyasa musamman masu shirin neman takarar shugaban kasa na ci gaba da kokarin yada manufofinsu duk da ba a fara kamfen 2027 ba
- Wata kungiya ta yi ikirarin cewa Olawepo-Hashim, daya daga cikin masu neman mulki a PDP ya karbu a wurin jama'ar jihar Osun
- A cewar kungiyar, alkaluman da suka tattara sun nuna cewa sunan Olawepo-Hashim ya fi shahara a bakunan jama'a fiya da Tinubu a Osun
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Osun - Wata kungiyar magoya bayan Gbenga Olawepo-Hashim ta Kudu maso Yamma ta yi ikirarin cewa mutane sun fara sauka daga jirgin Bola Ahmed Tinubu a Osun.
Kungiyar mai suna 'South West Gbenga Hashim Solidarity Movement' ta ce a yanzu tana ganin wanda take goyon baya ya sha gaban Tinubu a bakunan jama'a a jihar Osun.

Source: Twitter
Shugaban kungiyar, Alhaji Abass Olaniyi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce Olawepo-Hashim, wanda ke neman takarar shugaban kasa a inuwar PDP, ya fi karbuwa a wurin al'ummar jihar Osun fiye da Shugaba Tinubu.
Yadda Olawepo-Hashim ya karbu a Osun
A cewarsa, sunan Olawepo-Hashim ya bazu cikin jama’ar jihar Osun wanda ke nuna irin yadda yan Najeriya suka karbe shi hannu biyu tun kafin zaben 2027.
Duk da cewa Bola Tinubu ya taɓa zama gwamnan jihar Legas, iyayensa daga jihar Osun suka fito.
Olaniyi ya bayyana cewa sunan Olawepo-Hashim ne a bakin jama’ar jihar a kullum, har ma wasu na barkwanci cewa zai iya lashe zaben gwamna a Osun cikin sauƙi, in ji rahoton The Nation.
'Ana ambatar dan PDP fiye da Tinubu a Osun'
“Abin da aka fara da niyyar ɓata suna yanzu ya zama hanyar tallata shi kyauta. Dr. Hashim shi ne fuskar siyasar akida a Najeriya.
"’Yan PDP a jihar Osun suna tare da shi da Gwamna Ademola Adeleke za su taimaka wajen ceto Najeriya nan da shekarar 2027.
"Yan adawa da suka cika kafafen sada zumunta da ƙarya domin kawo rikici, sai dai sun ƙarfafa haɗin kanmu tare da ɗaga martabar Dr. Hashim a duk fadin yankin Kudu maso Yamma."
- Alhaji Abass Olaniyi.

Source: Twitter
Shin Olawepo-Hashim zai iya kai labari a 2027?
Olaniyi ya bayyana cewa dubban ’yan Najeriya suna bincike a kan Dr. Gbenga Hashim a yanar gizo suna gano tarihin jarumtaka, gaskiya da hangen nesansa.
“A fili yake cewa Allah na tare da shi. Ba abin da zai iya hana ƙaddara. Abin da makiya suka yi da niyyar sharri ya zama hanyar yaɗa saƙonsa tare da bayyana shi a matsayin amintaccen da Najeriya ke jira.
"Idan PDP ta dunkule wuri ɗaya, tare da goyon bayan jama’a, Dr. Gbenga Olawepo-Hashim na iya zama shugaban ƙasa na gaba a shekarar 2027,” in ji shi.
Fasto ya yi hasashen nasarar Tinubu a 2027
A wani labarin, kun ji cewa wani babban fasto a Legas, Apostle Victor Oku, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu ne zai samu nasara a zaben 2027.
Ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake cin zabe duk da hakadar da wasu manyan 'yan siyasa a kasar ke yi a kansa gabaninn2027.
Apostle Oku ya yarda cewa ana fama da matsaloli a yanzu, amma yance Ubangiji zai juya lamarin nan ba da jimawa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


