Shirin Kifar da Tinubu: Peter Obi Ya Gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Shirin Kifar da Tinubu: Peter Obi Ya Gana da Goodluck Jonathan a Abuja

  • Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan da Peter Obi sun yi ganawar sirri a birnin tarayyawatau Abuja
  • Rahotanni sun bayyana cewa Obi ya tabbatar da cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan halin da ƙasar ke ciki
  • Ganawar ta jawo ce-ce-ku-ce kan yiwuwar sabon haɗin gwiwar siyasa kafin 2027 domin kifar da Bola Ahmed Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - 'Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya gana da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Abuja a ranar Alhamis.

Ganawar, wacce aka gudanar a sirrance, ta haifar da mahawara kan makomar siyasar Najeriya a gabanin zaben 2027.

Obi yana gaisawa da Goodluck Jonathan yayin da suka hadu a Abuja
Obi yana gaisawa da Goodluck Jonathan yayin da suka hadu a Abuja. Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Obi ya sanar da ziyarar a shafinsa na X, inda ya bayyana Jonathan a matsayin babban ɗan’uwa, dattijo mai hangen nesa, kuma jagora.

Kara karanta wannan

Tinubu da kansa ya fadi abubuwan da ya tattauna da shugaban Kasar Faransa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Obi ya tattauna da Jonathan?

Peter Obi ya ce ganawar ta kasance mai albarka, inda suka tattauna kan halin da ƙasar ke ciki da kuma hanyoyin magance ƙalubale.

Kodayake ba a bayyana cikakken bayanin tattaunawar ba, lokaci da yanayin ganawar sun jawo hankalin jama’a, musamman duba da yadda ake ta tattaunawa kan halin da kasa ke ciki.

A sakon da ya fitar, Obi ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasar ya kasance mutum mai nuna dattaku a lamura.

A matsayin wanda ya fito na uku a babban zaben 2023, Obi na cigaba da tattaunawa da manyan ‘yan siyasa domin karfafa alaka da fahimtar juna kan makomar Najeriya.

Matsayin Jonathan a siyasar Najeriya

Jonathan ya jagoranci Najeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015, inda a yanzu ake masa kallon mai son zaman lafiya a Afrika.

Ganawarsa da Obi ta zo ne a daidai lokacin da jam’iyyar PDP ke kokarin farfadowa kafin 2027, inda aka zuba ido kan yiwuwar takararsa ko goyon bayansa ga wani ɗan takara daga Kudu.

Kara karanta wannan

Majalisa na barazanar hada minista da Tinubu kan 'raina' 'yan Najeriya da suka yi hadari

A shekarar 2015, Mai girma Jonathan ya nada Peter Obi a matsayin shugaban majalisar da ke kula ayyukan SEC a Najeriya.

Obi ya samu mukamin a hukumar mai alhakin kula da kasuwar hannun jari ne kusan wata guda kafin shugaban kasar ya sauka.

Me ake tsammani bayan ganawar?

Punch ta wallafa cewa ganawar ta ƙara ɗaga zancen yiwuwar sabon haɗin gwiwar siyasa tsakanin manyan ‘yan siyasa a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa PDP na ƙoƙarin dawo da Obi cikin jam’iyyar, ganin cewa shi ne ɗaya daga cikin manyan jiga-jigai da za su iya kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Ganawar sa da Jonathan ta biyo bayan jerin ganawa da yake yi da wasu fitattun ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki, abin da ya nuna shirin da ake yi na sabon tsarin siyasa.

Magoya bayan Obi ba su magantu ba

Ƙoƙarin samun karin bayani daga tsohon kakakin yakin neman zaben Obi, Dr. Yunusa Tanko, da kuma shugabannin ƙungiyar Obidient Movement bai samu nasara ba.

Kara karanta wannan

Kungiyar TUC ta ja daga, ta ba gwamnatin Tinubu kwanaki 14 ta janye harajin fetur

An gaza samun amsa daga gare su ne bayan ba su dauki kiran da daka musu ta wayar tarho ba kuma ba su yi martani ba bayan saƙonnin da aka tura musu.

LP ta ce za ta hana Peter Obi takara

A wani rahoton, kun ji cewa tsagin jam'iyyar LP ya bayyana cewa ba zai ba Peter Obi takara ba a zaben 2027.

Hakan na zuwa ne yayin da Peter Obi ya sha nanata cewa zai shiga takarar zaben 2027 domin bugawa da Bola Tinubu.

Peter Obi da ya kasance cikin masu shirin hadaka a jam'iyyar ADC bai fito ya yi martani kan maganar ba har yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng