Babbar Magana: Malami Ya Zargi Gwamna da Wasu Yan Siyasa da Alaka da 'Yan Ta'adda
- Abubakar Malami ya shigar da korafi gaban mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro da shugabannin hukumomin tsaron cikin gida
- Tsohon ministan ya zargi Gwamna Nasir Idris da kokarin dauko sojojin haya daga waje, da shigo da 'yan daba cikin Kebbi don danne 'yan adawa
- Malami SAN ya kuma yi zargin cewa gwamnan da wasu 'yan siyasa da ke tare da shi su na da alaka da kungiyar ta'addanci ta Lakurawa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Tsohon Ministan Shari’a na Tarayya kuma Antoni Janar, Abubakar Malami, SAN, ya kai korafin Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi gaban jami'an tsaro.
Malami, wanda shi ne jagoran jam’iyyar ADC a jihar Kebbi, ya shigar da korafi kan abin da ya bayyana a matsayin shirin da ake yi na tayar da hankali jama'a a jihar.

Kara karanta wannan
Ganduje ya kafa kwamiti, zai binciki gwamnatin Kano kan korar kwamandojin Hisbah 44

Source: Twitter
A cewar rahoton Leadership, tsohon ministan ya zargi Gwamna Nasir da yunkurin shigo da ‘yan dabar siyasa, sojojin haya daga ƙasashen waje da makamai cikin Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malami ya kai korafin gwamnan Kebbi
Malami ya aika da ƙorafin nasa ga Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP), Daraktan DSS, da kuma Shugaban Hukumar Tsaro Ta NSCDC.
A cikin ƙorafin mai kwanan watan 10 ga Satumba, 2025, Malami ya zargi gwamna da hannu a kulla makirci da nufin danne 'yan adawa a jihar Kebbi.
Malami ya yi ikirarin cewa wasu ‘yan siyasa sun dauko sojojin haya daga Jamhuriyar Nijar, tare da samar musu da makamai ta haramtattun hanyoyi.
Ya ce an fara baza su cikin al’umma domin kai hari ga mutane, tsoratar da yan adawa, da kuma lalata zaman lafiya a jihar Kebbi.
Zarge-zargen Malami kan Gwamna Nasir
Ya bayyana cewa wannan barazana da ya hango ba zato ba ne, yana da kwararan hujjoji da ya tattara a sirrance da kuma wadanda ya gane ma idonsa.
A cewarsa, a ranar 1 ga Satumba, 2025, wasu yan daba dauke da makamai da ke cin karenau babu babbaka, sun kai masa hari shi da magoya bayansa.
Ƙorafin Abubakar Malami ya kuma zargi Gwamna Nasir Idris da mukarrabansa da da hannu wajen kai masa hari, tare da yin zargin cewa suna da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa.

Source: Facebook
Matakin da tsohon ministan ya nemi a dauka
Malami ya bayyana lamarin a matsayin "batun gaggawa na ƙasa” wadda ta zarce siyasar cikin gida, ya zama barazana ga Najeriya da zaman lafiya na cikin gida.
Ya roƙi NSA da sauran shugabannin tsaro su ɗauki mataki cikin gaggawa ta hanyar haɗa kai wajen tsaurara tsaro a yankunan kan iyaka domin hana shigo da sojojin haya da makamai.
Tsohon ministan ya kuma roki su kaddamar da babban bincike kan zargin haɗin alaka tsakanin jami’an gwamnatin Kebbi da ƙungiyoyin ta’addanci, in ji rahoton Daily Post.
Gwamnatin Kebbi ta musanta ikirarin Abubakar Malami
Kuna da labarin cewa, gwamnatin jihar Kebbi ta nesanta kanta da harin da tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya ce an kai masa da tawagarsa.
Hadimin gwamnan Kebbi, Yahaya Sarki ya ce hujjojin da ke hannunsu za su tabbatar da cewa Malami da mutanensa ne suka fara yunkurin tayar da rikici.
Yahaya ya bayyana mamakinsa a kan yadda Abubakar Malami SAN ya jefa kansa a cikin rigima da da 'yan daba, lamarin da ya ce zai iya haifar da matsala.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

