Yana Kukan An Soma Kamfen 2027 tun Yanzu, Magoya Baya Sun Fara Tallata Tinubu

Yana Kukan An Soma Kamfen 2027 tun Yanzu, Magoya Baya Sun Fara Tallata Tinubu

  • A 'yan kwanakin nan aka ji shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na kokawa cewa 'yan siyasa sun fara kamfen 2027 da wuri
  • Wata kungiya a jihar Ondo da ke samun goyon baya daga ministan cikin gida, Dr. Tunji-Ojo ta fara tallata Bola Tinubu gida-gida
  • A cewar kungiyar, za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin Tinubu ya yi tazarce domin ya ci gaba da ayyukan alherin da ya fara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - ‘Yan jam’iyyar APC a jihar Ondo ƙarƙashin inuwar kungiyar Asiwaju Mandate Group (AMG) sun ƙaddamar da yakin neman zaɓe na gida-gida.

'Yan kungiyar sun kaddamar da fara shiga gida-gida domin neman goyon bayan yan Najeriya game da tazarcen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Wasu gwamnoni za su sauya sheka zuwa jam'iyyar APC kafin zaben 2027 a Najeriya'

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a lokacin da ya kai ziyarar aiki jihar Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Kungiyar AMG ta kudiri aniyar tallata Tinubu ne bisa goyon bayan da take samu daga Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, in ji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An fara tallata Tinubu gida-gida a Ondo

Ta bayyana cewa manufarta ita ce tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya koma mulki a karo na biyu domin ci gaba da aiwatar da manufar Renewed Hope da sauran shirye-shiryen da suka shafi talakawa.

Shugaban kungiyar, Muyiwa Asagunla shi ne ya fadi haka a wurin rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi da mazabu na AMG da aka gudanar a Ikare-Akoko, karamar hukumar Akoko ta Arewa-Maso-Yamma, ranar Laraba,

Muyiwa Asagunla ya ce an riga an fara aikin zuwa wurin jama’a gida-gida domin ƙarfafa masu gwiwa su ci gaba da goyon bayan Tinubu da jam’iyyar APC.

Ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin “mai gina mutane na gaskiya” wanda ya nuna azama da ƙoƙari wajen inganta rayuwar al’umma ta hanyar shirye-shiryen tallafi, Arise News ta rahoto

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan Tambuwal ya zargi Tinubu da shirin ruguza 'yan adawa

Kungiyar AMG ta shirya tarawa APC kuri'u

A cewarsa, wajibi ne APC ta ci zaɓen da ke tafe, inda ya jaddada cewa AMG ta kuduri aniyar “wayar da kai da kuma faɗakar da masu kaɗa kuri’a tun daga matakin unguwanni zuwa sama."

Asagunla ya yi kira ga sababbin shugabannin da aka rantsar su maida hankali wajen tallata Tinubu gida-gida kamar yadda tsarin AMG na jiha ya tanada ƙarƙashin jagorancin Dr. Tunji-Ojo,

Shugaba Bola Tinubu.
Hoton mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Wadanda suka halarci taron sun kunshi fitattun jagororin APC da suka haɗa da Gani Amuda, sakataren APC na shiyyar Ondo ta Arewa; Deni Akerele, tsohon ɗan majalisar wakilai; Liadi Ekunnusi; da Olu Arowolo, tsohon shugaban Akoko.

Tinubu ya samu goyon baya daga Bayelsa

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Bayelsa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake yin takara a 2027.

Amma abin mamaki, wasu daga cikin kusoshin APC a jihar a Bayelsa kamar Karamin Ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri ba su halarci taron ba.

Kara karanta wannan

"A koresu": Kungiyar 'yan Arewa ta ba Tinubu shawara kan rashin tsaro

Rashin ganin ministan da kuma tsohon dan takarar gwamna, Cif David Lyon a taron da haifar da shakku kan hadin kan 'ya'yan APC a Bayelsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262