An Nemi Minista da Ɗan Takarar Gwamna, an Rasa a Taron Nuna Goyon baya ga Tinubu
- Jam'iyyar APC a jihar Bayelsa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin sake yin takara a 2027
- Amma abin mamaki, Ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da wani jigon jam'iyyar ba su halarci taron ba
- Rashin ganinsu a taron ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman da aka ji cewa Lokpobiri ne ya shirya taron, amma shi bai halarta ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayelsa – Jam’iyyar APC a jihar Bayelsa ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin ya yi tazarce a babban zaben 2027.
Amma abin mamaki, kusoshin jam'iyyar a jihar, karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da tsohon dan takarar gwamna a 2019, Cif David Lyon ba su halarci taron ba.

Source: Facebook
Minista ya ki halartar taron APC a Bayelsa
A cewar rahoton The Punch, rashin ganin karamin ministan da tsohon dan takarar gwamnan a wajen taron ya haifar da tambayoyi kan hadin kan APC a Bayelsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta nuna goyon bayanta ga tazarcen Tinubu ne a taron masu ruwa da tsaki karo na 12 da aka gudanar a Yenagoa ranar Talata, inda manyan jiga-jigan jam’iyyar suka halarta.
Mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (Kudu), Cif Emma Eneukwu ne ya wakilci shugaban jam'iyyar na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a wajen taron.
Ambasada Philip Ikrusi ne ya gabatar da kudurin nuna goyon baya ga Tinubu, inda tsohon dan majalisa, Preye Oseke, ya mara masa baya.
Sylva ya magantu kan rashin ganinsu minista
Ambasada Ikrusi ya ce:
“Na dauki wannan mataki ne saboda jagoranci mai nagarta da hangen nesa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna tun bayan hawansa mulki a 2023.”
Ya yaba da sauye-sauyen gwamnati, kokarin hada kan kasa, karfafa dimokuradiyya da kuma nadin ‘yan Bayelsa a muhimman mukamai, inji rahoton This Day.
Tsohon gwamnan Bayelsa kuma tsohon ministan albarkatun man fetur, Cif Timipre Sylva, ya nuna damuwarsa kan rashin halartar Lokpobiri da Lyon, yana mai cewa:
“Abin da kawai muke bukata shi ne goyon bayan shugabannin jam’iyya na kasa. Idan muka samu hakan, to wannan jam’iyyar za ta dawo da karfinta a jihar nan."

Source: Facebook
Rikicin cikin gida ya ci gaba a APC
Sai dai duk da nuna goyon baya ga Tinubu, rashin Lokpobiri da Lyon a taron ya sake tona rikicin cikin gida da ya mamaye APC a Bayelsa.
Mun ruwaito cewa an taba dakatar da kusoshin biyu tare da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Werinipre Seibarugu, da wasu magoya bayansu kan rikicin neman ikon jam’iyya.
Kodayake daga baya an janye dakatarwar da aka yi masu, bisa alkawarin yin zaman sulhu, amma ana ganin har yanzu ba a warware rikicin shugabancin ba.
Wata majiya ta ce ministan ne ma ya shirya taron masu ruwa da tsakin na ranar Talata, amma kuma shi bai halarta ba, abin da ya jefa mutane a mamaki.
Rigima ta barke a APC kan korar Lokpobiri
Tun da fari, mun ruwaito cewa, APC ta rikice a jihar Bayelsa bayan da aka dakatar da Ministan man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri daga jam'iyyar.

Kara karanta wannan
Romon siyasa: Kansila ya naɗa sababbin hadimai 18, ya raba masu wurin aiki a Kaduna
Wasu shugabannin APC a shiyyar Kudu maso Kudu sun ce hassada da tsantsar bakin ciki ne suka sanya aka kori ministan, kuma matakin ya saba doka.
Babban lauyan APC a Kudu maso Kudu, Chukwuemeka Ogbuobodo ya ce shugabannin jam'iyya na kananan hukumomi ba su da izinin korar ministan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

