Kwankwaso Ya Fara Shirin Zaben 2027 yayin da Ake Rufe Zancen Komawarsa APC
- Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugabannin jam’iyyar NNPP a jihar Cross River
- Sanata Kwankwaso ya bada sharwari ga 'ya'yan jam'iyyar yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027
- Shugaban NNPP na jihar ya bayyana yadda su ka ji a ransu kan ziyarar da tsohon dan takarar shugaban kasan ya kai musu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Calabar, jihar Cross River – Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara jihar Cross River.
Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugabannin jam’iyyar NNPP a jihar Cross River domin tsara dabarun shiga zaben 2027.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa Kwankwaso ya gana da shugabannin jam'iyyar ne a birnin Calabar, ranar Talata, 9 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan
Rikicin NNPP: Rigima ta barke a jam'iyyar Kwankwaso bayan korar da dan Majalisa a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya sanya hotunan taro a shafinsa na X.
Rabiu Kwankwaso ya ba 'yan NNPP shawara
A yayin taron, Kwankwaso ya bukaci ‘ya’yan NNPP su bai wa hadin kai muhimmanci tare da karfafa gwiwar jam’iyyar a fadin jihar.
"Ina godiya ga shugabanni da mambobin NNPP a jihar Cross River. Mun yi farin cikin yadda kuka tarbe mu, da kuma yadda shugabancin jam’iyya yake tafiya."
"Zan kara karfafa gwiwarku ku dage wajen ganin an samu hadin kai a cikin jam’iyyar.”
- Rabiu Musa Kwankwaso
Me Kwankwaso ya ce kan zaben 2027
Ya kara da cewa, dole ne jam’iyyar ta tashi tsaye da zuciya daya idan tana da burin lashe zaben jiha da na kasa a 2027.
"Na gode da abin da kuka yi a zaben 2023 da ya gabata. Ina kira gare ku da ku kara jajircewa domin da ikon Allah jam’iyyarmu, NNPP, za ta yi nasara a Cross River da ma kasa baki daya."
"Ku tabbatar da hadin kai musamman yanzu da muka bude babban ofishi a Calabar da kuma a wasu kananan hukumomi a fadin jihar. A madadin tawagata, muna muku godiya, Allah ya saka da alheri."
- Rabiu Musa Kwankwaso

Source: Twitter
Shugaban NNPP na jiha ya yabawa Kwankwaso
Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Tony Odey, ya bayyana ziyarar Kwankwaso a matsayin abin da ya kara musu kwarin gwiwa.
"Mun tattaro shugabanni daga fannoni daban-daban don mu tattauna muhimman al’amura, mu bayyana ra’ayoyi sannan mu samo sabuwar hanyar samun ci gaba. Shawarwarinka da jagorancinka za su kara mana karfi.”
- Tony Odey
Ya kuma yaba da kokarin kwamitin tuntuba karkashin jagorancin Alhaji Ahmed Bichi, bisa samar da ofishin jam’iyya da kuma bayar da mota, wanda ya ce hakan ya zama abin kishi ga sauran jam’iyyu a jihar.
Bugu da kari, ya bayyana cewa ban da babban ofishin jiha da ke Calabar, shugabancinsa ya riga ya biya kudin ofisoshi a kananan hukumomi biyar da ke yankin Arewacin jihar, inda ake shirin yin musu fenti da launin jam’iyya.
Kwankwaso ya gana da 'yan kasuwar Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya karbi bakuncin 'yan kasuwar Arewa masu sana'ar lemu a jihar Benue.

Kara karanta wannan
2027: 'Yan siyasan Arewa da za su rasa damar takara saboda kai tikitin PDP zuwa Kudu
Kwankwaso ya gana da 'yan kasuwar ne a wani taron da aka shirya a jihar Nasarawa mai makwabtaka da Benue.
'Yan kasuwar sun mika kokensu ga Kwankwaso, inda suka gaya masa cewa sana'arsu ta durkushe saboda matsalolin da su ke fuskanta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
