'Wasu Gwamnoni Za Su Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar APC kafin Zaben 2027 a Najeriya'
- Jam'iyyar APC na fatan kara karbar wasu gwamnoni da za su baro jam'iyyunsu domin shiga tafiyar Shugaba Bola Tinubu kafin 2027
- Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ce manyan yan siyasa na shiga jam'iyya mai mulki ne saboda ci gaban Najeriya
- Yilwatda ya ce Shugaba Tinubu na kokarin sauke nauyin da ke kansa, shiyasa bai damu da masu babatu kan shirin kalubalantarsa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa - Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa nan gaba wasu gwamnoni za su sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki kafin zaɓen 2027.
Farfesa Yilwatda ya bayyana haka ne a Yenagoa, babban birnin Bayelsa, a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar karo na 12.

Source: Twitter
Daily Trust ta tattaro cewa a taron, masu ruwa da tsakin APC na Bayelsa sun nuna goyon baya ga tazarcen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC za ta samu karin gwamnoni kafin 2027
Da yake jawabi a wurin taron, Farfesa Yilwatda ya ce salon shugabancin Tinubu ke kara jawo hankalin gwamnoni da sanatoci zuwa jam'iyyar APC.
A cewarsa, wasu karin gwamnoni da yan Majalisar Tarayya za su shiga jirgin APC domin tabbatar da nasarar Shugaba Tinubu a zaben 2027.
“Kofarmu a buɗe take, ƙarin gwamnoni, sanatoci da ‘yan majalisar wakilai za su taho su shiga APC saboda nagartar shugabancin wanda muka zaba ya jagoranci ƙasa.
"Wasu na ƙoƙarin kalubalantar shugaban ƙasa a 2027, amma kowa ya sani idan zaki ba sa'an kananun dabbobi ba ne, shi yasa kuka ga shugaban kasa bai damu ba, yana gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali.
Vanguard ta tattaro cewa gwamnan jihar Delta, Rt. Hon Sheriff Oborevwore, da gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, sun bar PDP zuwa APC a watannin baya.
Me yasa manyan 'yan siyasa ke shiga APC?
Farfesa Yilwatda, wanda mataimakin shugaban APC na ƙasa (Kudu), Cif Emma Eneukwu, ya wakilta, ya ce gwamnoni da dama sun gane nagartar Bola Tinubu.
Ya ce gwamnonin Kudu maso Kudu da wasu daga Kudu maso Gabas sun gane halin nagarta da hangen nesa na shugaban ƙasa, hakan ya sa suka bar jam’iyyunsu suka shiga APC.
"Abin da ya sa kuke ganin gwamnoni da yan Majalisa na shigowa APC shi ne suna so a hada hannu wuri guda domin ciyar da Najeriya gaba."

Source: Twitter
Yilwatda ya yi kira ga mambobin APC a Bayelsa da su kasance tsintsiya ɗaya, su yi aiki tare, domin jam’iyyar ta samu galaba a zaɓen 2027.
APC ta musanta ikirarin Sanata Tambuwal
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta waiwayi Sanata Aminu Tambuwal bayan ya soki gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
APC mai mulki ta yi fatali da wasu kalamai da Tambuwal ya fada kan Tinubu, tana mai bayyana maganganun tsohon gwamnan da karya mara tushe.
Tun farko Tambuwal ya zargi Shugaba Tinubu da hannu a duk rigingimun cikin gida da suka hana jam'iyyun adawa zaman lafiya a kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

