"Ta Mutu": Sanata Dino Melaye Ya Fadi Masu Ikon Juya Jam'iyyar PDP

"Ta Mutu": Sanata Dino Melaye Ya Fadi Masu Ikon Juya Jam'iyyar PDP

  • Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Sanata Dino Melaye, ya yi maganganu kan PDP
  • Sanata Dino Melaye ya nuna cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta kai matakin da an shafe babinta don ta mutu murus
  • Hakazalika 'dan siyasar ya bayyana fatan da yake da shi kan jam'iyyar ADC a zaben shekarar 2027 da ake tunkara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon sanata mai wakiltar yankin Kogi ta Yamma a majalisar dattawa, Dino Melaye, ya caccaki jam'iyyar adawa ta PDP.

Dino Melaye ya bayyana cewa PDP “ta mutu kuma an birne ta”, yana zargin cewa jam’iyyar yanzu tana karkashin ikon APC.

Dino Melaye ya ragargaji jam'iyyar PDP
Hoton Sanata Dino Melaye yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Senator Dino Melaye
Source: Twitter

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne yayin da ake tattaunawa da shi a tashar Arise Tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dino Melaye ya ce jam'iyyar PDP ta mutu

Kara karanta wannan

'Sanatoci da 'yan Majalisar Wakilai da dama sun shiga jam'iyyar hadaka, ADC'

Dino Melaye ya kawar da duk wani fatan farfadowar jam’iyyar adawan, inda ya ce ba ta da ikon gudanar harkokinta cikin 'yanci.

"Ban da Ubangijinmu Yesu Kiristi, babu wani matacce da zai iya tashi. PDP ta mutu kuma an birne ta."
"An sayar da jam’iyyar, ba ni da tabbacin ko sun karɓi takardar shaidar biyan kuɗin. Abin da kuke da shi yanzu shi ne PDP wanda APC ke iko da ita."

- Dino Melaye

Dino Melaye, wanda a baya ya tsaya takarar gwamna a karkashin PDP, ya zargi wasu wakilan APC da shiga cikin jam’iyyar tare da jagorantar harkokinta daga fadar shugaban kasa.

"Jam’iyya ce da ake tafiyar da ita daga Villa. Na taɓa faɗi cewa a gani na wakilan APC ne ke gudanar da harkokin PDP."

- Dino Melaye

Dino Melaye yana alfahari da ADC

Sai dai tsohon sanatan ya bayyana cewa shi yanzu ba ɗan PDP ba ne, domin ya koma ADC wadda ya bayyana a matsayin jam'iyyar da za ta iya kayar da gwamnatin APC ta Shugaba Bola Tinubu a babban zaɓen da ake tunkara.

Kara karanta wannan

Dalung: Ministan Buhari ya fadi shirin jam'iyyar ADC kan zaben 2027

Dino Melaye wanda ya yi takarar gwamnan Kogi kwanan nan a jam'iyyar PDP ya bayyana yana alfahari da ADC a yau.

"Ni cikakken ɗan jam’iyyar ADC ne, kuma da ikon Allah, ita ce jam’iyyar da za ta kori Tinubu tare da fitar da APC daga Villa a ranar 29 ga watan Mayu, 2027."

- Dino Melaye

Dino Melaye ya ce PDP ta koma karkashin APC
Hoton Sanata Dino Melaye yana jawabi Hoto: Senator Dino Melaye
Source: Facebook

Dino Melaye ya ba 'yan Najeriya shawara

Yayin da ya karkatar da tattaunawar daga rikicin cikin gida na PDP, Melaye ya roki ‘yan Najeriya da su mayar da hankali kan manyan matsalolin da suka addabi kasar nan.

"Akwai matsaloli masu tsanani da suka addabi wannan kasa: yunwa, rashin abinci mai gina jiki, rashin ingantaccen mulki, da kuma jagoranci mara kyau."
"Waɗannan su ne abubuwan da nake ganin ya kamata mu tattauna, ba jam’iyya matacciya ba."

- Dino Melaye

Sanata Dino Melaye ya fice daga PDP

A baya rahoto ya zo cewa tsohon dan takarar gwamnan jihar Kogi a karkashin inuwar PDP, Sanata Dino Melaye, ya fice daga jam'iyyar.

Sanata Dino Melaye ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP ne a cikin wata wasika da ya rubuta tare da rattabawa hannu.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan Tambuwal ya zargi Tinubu da shirin ruguza 'yan adawa

Tsohon sanatan ya bayyana cewa PDP mai alamar laima ta gaza domin ba za ta iya ceto Najeriya daga cikin halin da take ciki ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng