'Sanatoci da Yan Majalisar Wakilai da Dama Sun Shiga Jam'iyyar Hadaka, ADC'
- Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye ya yi ikirarin cewa daruruwan sanatoci da yan Majalisar wakilai sun shiga ADC
- Dino Melaye ya ce jam'iyyar ADC na kara karfi a kowace rana kuma a shirye take ta karbe mulkin Najeriya daga hannun APC a 2027
- Ya kuma soki zaben cike gurbin da aka gudanar kwanakin baya a wasu jihohi, yana mai cewa ba sahihin zabe aka yi ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi - Tsohon dan majalisar dattawa daga jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa jam’iyyar hadaka, ADC, na ƙara ƙarfi a siyasar Najeriya.
Melaye, tsohon dan takarar gwamnan Kogi a inuwar jam'iyyar PDP ya yi ikirarin cewa manyan 'yan siyasa da masu mulki na ci gaba da tururuwar shiga ADC.

Source: Facebook
Tsohon sanatan Kogi ta Yamma ya yi wannan bayani ne a cikin wata hira da ya yi da tashar Arise News a shirin PrimeTime.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce ADC na samun ci gaba da sauri kuma tana shirye-shiryen karɓar mulki daga hannun APC a shekarar 2027.
Melaye ya yi ikirarin 'yan majalisa sun shiga ADC
Ya yi ikirarin cewa sanatoci da 'yan Majalisar Wakilan Tarayya sun rungumi tafiyar ADC, yana mai cewa sun shirya tsaf domin karbar ragamar Najeriya.
“Kullum muna da sababbin mutane da ke shiga ADC. A halin yanzu muna da sama da Sanatoci 100, tsofaffi da masu ci, da kusan ‘yan majalisar wakilai 400, tsofaffi da masu ci.
"Sannan muna da tsofaffin gwamnoni da suka shiga wannan tafiya, jam’iyyar ADC tana girma cikin sauri kuma tana kara karfi fiye da tunani," In ji Dino.
Sai dai babu wani rahoto da ya tabbatar da wannan ikirari na Dino Melaye game da adadin yawan sanatoci da yan Majalisar Wakilan da suka rungumi ADC.
Tsofaffin 'yan Majalisa suna da karfi a siyasa?
Da aka tambaye shi kan tasirin tsofaffin ‘yan majalisa a siyasar Najeriya, Melaye ya ce:

Kara karanta wannan
Romon siyasa: Kansila ya naɗa sababbin hadimai 18, ya raba masu wurin aiki a Kaduna
“Ya danganta da yadda mutum yake da karfi a mazabarsa. A gaskiya da yawa daga cikin ‘yan majalisar tarayya na yanzu suna bin jagoranci tsofaffin ‘yan majalisa ne."
Melaye, wanda ya taba zama ɗan majalisar wakilai, ya jaddada cewa ADC na shirye-shiryen fatattakar APC daga fadar shugaban kasa a 2027," in ji rahoton Leadership.
“Ni cikakken ɗan ADC ne, kuma wannan ce jam’iyyar da za ta kori APC daga Aso Rock a ranar 29 ga Mayu, 2027 da ikon Allah.”

Source: Facebook
Dino Melaye ya soki zaben cike gurbi
Yayin da yake tsokaci kan zabubbukan cike gurbi da aka kammala inda APC ta lashe mafi yawan kujeru, Melaye ya yi watsi da sakamakon, yana kiran shi da karya.
“Ba zabe aka yi ba. Amma ina tabbatar muku cewa 2027 ba za ta kasance haka ba. ‘Yan Najeriya sun kara wayewa yanzu," in ji shi.
Melaye ya soki yawan karbo bashin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayyana damuwa kan yawan cin bashi da gwamnatin Tinubu ke yi a Najeriya.

Kara karanta wannan
Kusan watanni 2 bayan ya rasu, an dauko batun ayyuka da Buhari ya gaza yi a Arewa
Melaye ya yi gargadi cewa idan ba a kula ba, Tinubu na iya fara neman bashi daga manyan kamfanonin kudi na kasar, kamar Opay da Moniepoint.
Ya kuma soki matakin Tinubu na sayen jirgin sama da jirgin ruwa a daidai lokacin da yan Najeriya ke fama da yunwa da talauci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
