Ministan Buhari Ya Gaji da Zama haka, Zai Nemi Takarar Gwamna karkashin APC
- Tsohon Ministan Sadarwa a Najeriya ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamna a 2027, yana cewa ba mai kwarewarsa
- Adebayo Shittu ya ce shi ne mafi cancanta domin ya fara siyasa tun 1979 a Majalisar Oyo, sannan ya rike mukamai da dama
- Shittu wanda dan asalin Oke-Ogun ne ya jaddada cewa yankinsa bai taba samun gwamna ba, yana mai cewa lokacinsu ya yi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Tsohon Ministan Sadarwa kuma jigo a jam’iyyar APC ya nuna kwadayinsa a fili kan neman takarar gwamna.
Adebayo Shittu ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar gwamna a Oyo 2027, yana cewa babu kamarsa wajen kwarewa da hangen nesa.

Source: Facebook
2027: Tsohon minista zai nemi takarar gwamna
Shittu ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin wata tattaunawa ta musamman a shirin Frontline na Eagle 102.5 FM, Ilese-Ijebu, wanda TheCable ta bibiya.

Kara karanta wannan
Kusan watanni 2 bayan ya rasu, an dauko batun ayyuka da Buhari ya gaza yi a Arewa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana kansa a matsayin mafi cancanta, inda ya ambaci gogewarsa ta siyasa wacce ta wuce shekaru 40, tun daga lokacin da aka zabe shi a 1979.
Rahoton Daily Post ya ce Shittu ya fara siyasa a 1979 lokacin da aka zabe shi a tsohuwar Majalisar dokokin Oyo yana dan shekara 26 kacal.
A wancan lokacin, an nada shi Kwamishinan sadarwa, al’adu da harkokin cikin gida kafin daga bisani ya zama Ministan Sadarwa a 2015 zuwa 2019 a karkashin mulkin Muhammadu Buhari.
Ya ce:
“A yau ni ne kadai nake da kundin manufofi na abin da nake son yi idan na shiga gidan gwamnati, na shirya tsaf don mulki.
“Ko da na samu dama a yau, na riga na san abin da zan yi. Ina so in sauya jihar Oyo yadda ba a taba gani ba.”

Source: UGC
Korafin rashin adalci daga bakin Adebayo Shittu
Dan asalin Oke-Ogun din ya ce yankinsa na fama da wariya wajen samun mulki, yana mai kira da a ba su dama a karon farko.
Ya kara da cewa:
“Gaskiyar magana ita ce, Ibadan cikin shekaru 30 zuwa 40 ta samar da gwamnoni guda shida, Ogbomosho ta samar da daya, amma Oke-Ogun bai taba samu ba.
“Dole a kawo sauyi, ba Ibadan kadai kullum ba, dimokuradiyya muke ciki, ba mulkin kama-karya ba.”
Tsohon minista, Adebayo Shittu mai shekaru 72 ya yi watsi da maganar tsufa inda ya ce shekaru lambobi ne kawai, a gwada shi wurin basira da kuzari.
“Ina da karfi kamar kowane mutum na shekaruna, har ma da yawa, shekaru ba za su hana ni mulki ba.”
- Adebayo shittu
Tsohon minista ya caccaki masu sukar shari'a
A baya, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kafa kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, yana cewa jahilci ne ke haddasa hakan.
A cewarsa, kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’in addini a wasu jihohi ba tare da haddasa wata matsala ba.
Ya kara da cewa Musulmi suna da ’yancin gudanar da harkokinsu bisa doka ta shari'a, don haka gwamnati ba ta da ikon hana su yin hakan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
