Jam'iyyar APC ba ta da wata marabar akida da manufofi da PDP - Adebayor Shittu

Jam'iyyar APC ba ta da wata marabar akida da manufofi da PDP - Adebayor Shittu

Adebayo Shittu, tsohon ministan sadarwa, ya bayyana jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) a matsayin iri daya da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bangaren akida.

A cewar Shittu, wanda ya riki mukamin minista a mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari na farko, APC da PDP na da kamanceceniya ta fuskancin akidarsu wajen tafiyar da gwamnati.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa tsohon ministan wanda ya yi magana a wani taro da yan jarida suka shirya a jihar Osun, ya kara da cewa APC na iya fuskantar rikici gabannin 2023.

Ya yi hasashen cewa APC na iya fuskantar matsala wajen samun kuri’u masu yawa kamar yadda ya samu a zaben 2019 a zabe na gaba.

An tattaro cewa ya tabbatar da cewar akwai matsala a cikin jam’iyyar sannan cewa wannan zai sa da wuya jam’iyyar ta samu goyon bayan yan Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Albashi na duk wata N54 ne a matsayin malamin makaranta - Sanata Wamakko

Ya zargi Ajimobi da muzgunawa kuirinsa na son zama gwamnan jihara 2019 inda ya kara da cewa gwamnoni basu da hujjar satar kudaden jama'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel