Dalung: Ministan Buhari Ya Fadi Shirin Jam'iyyar ADC kan Zaben 2027

Dalung: Ministan Buhari Ya Fadi Shirin Jam'iyyar ADC kan Zaben 2027

  • Jam'iyyar ADC ta zama sabuwar amarya da ake rububi a fagen siyasar Najeriya yayin da ake tunkarar zaben shekarar 2027
  • Solomon Dalung wanda ya yi minista a gwamantin marigayi Muhammadu Buhari, ya tabo batun shirin jam'iyyar kan shiga babban zaben
  • Tsohon ministan ya nuna cewa ADC a shirye take ta shiga zaben 2027 a yankurin da 'yan hadaka suka ce suna yi don ceto Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi magana kan shirin jam'iyyar ADC dangane da zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Solomon Dalung ya bayyana cewa ADC ta shirya sosai domin zaɓen shekarar 2027, duk da damuwar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta nuna kan rashin bin ka’idojin rajista daga jam’iyyar.

Solomon Dalung ya yi maganganu kan ADC
Hoton tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, yana jawabi Hoto: Solomon Dalung
Source: Getty Images

Solomon Dalung, wanda mamba ne a jam’iyyar ADC, ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa a shirin 'Morning Show' na tashar Arise Tv a ranar Litinin, 8 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Jam'iyyun siyasa 5 sun hadu don taimaka wa ADC a kifar da gwamnatin APC a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Solomon Dalung ya yi magana kan shirin ADC

Tsohon ministan ya yi watsi da fargabar cewa matsalolin rajista za su iya shafar shirye-shiryen jam’iyyar na shiga zaɓen 2027.

"ADC jam’iyya ce da aka yi wa rajista a Najeriya, wadda ta kwashe fiye da shekaru 19 tana wanzuwa."
"Jam’iyyar tana samun sauye-sauye inda aka shigo da 'yan hadaka. Saboda haka ba daidai ba ne a ce kungiya ce kawai."

- Solomon Dalung

Hukumar INEC ta ki yarda da shugabannin ADC

Hukumar INEC ta dage cewa har yanzu ADC ba ta cika wasu sharuddan da za su tabbatar da Sanata David Mark da Rauf Aregbesola a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa da sakatare ba.

Haka kuma ta yi gargadin cewa duk wasu takardu da su ka sa hannu ba su da inganci har sai an kammala tsarin rajistar.

ADC na son fafatawa a zaben 2025
Hoton jagororin jam'iyyar ADC a wajen kafa hadaka Hoto: @atiku
Source: Facebook

Dalung ya ce ADC za ta cika sharudda

Amma Solomom Dalung ya ce jam’iyyar ADC na aiki tukuru don cika waɗannan sharuddan na INEC.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan Tambuwal ya zargi Tinubu da shirin ruguza 'yan adawa

"Bukatun INEC tanadi ne na doka, kuma ADC ba ta da wani zaɓi illa ta bi. A bisa abin da na sani, shugabannin jam’iyya na aiki tukuru don tabbatar da an kammala hakan yadda ya kamata."

- Solomon Dalung

Tsohon ministan wasannin ya kara da cewa dole ne haɗakar da aka yi ta mutunta doka idan da gaske tana son ta taimaka wajen ceto kasar nan.

Solomon Dalung ya hango faduwar Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan wasanni a zamanin mulkin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Solomon Dalung ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai iya komawa Legas bayan kammala wa'adin mulkinsa na farko.

Jigon na jam'iyyar ADC ya nuna kwarin gwiwarsa kan cewa hadakar 'yan adawa za ta iya kawo karshen mulkin Shugaba Tinubu a zaben shekarar 2027

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng