Babbar Magana: Shugaba Tinubu Ya Kori Hadiminsa daga Aiki
- Hadimin mataimakin shugaban kasa kan harkokin tattalin arzikin zamani da kirkire-kirkire, Fegho John Umunubo ya rasa aikinsa
- Fadar shugaban kasa ta sanar da korar Umunubo a yau Litinin, 8 ga watan Satumba, 2025, ta ce matakin zai fara aiki ne nan take
- Sanarwar ta gargadi masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arzikin zamani cewa su guji mu'amala da shi domin ba shi da alaka da gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
State House, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kori wani daga cikin hadimansa, Fegho John Umunubo, wanda ke aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa.
Fadar shugaban kasa ta sanar da korar Fegho John Umunubo, mai taimaka wa mataimakin shugaban kasa kan harkokin tattalin arzikin zamani da kirkire-kirkire.

Source: Facebook
Hakan na kunshe a wata sanarwa da aka fitar a shafin X mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai da hulda da jama'a na fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye.

Kara karanta wannan
Romon siyasa: Kansila ya naɗa sababbin hadimai 18, ya raba masu wurin aiki a Kaduna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Dada Olusegun ya wallafa labarin a dandalinsa a yammacin ranar Litinin.
Tinubu ya sallami hadimin Kashim Shettima
A cewar sanarwar, daga wannan lokaci, Umunubo ba shi da wani matsayi a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma ba ya wakiltar fadar shugaban kasa a kowane irin aiki.
Fadar ta bukaci duka masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arzikin zamani da kirkire-kirkire, na cikin gida da waje, su gujewa mu'amala da Umunubo domin ba shi da alaka da gwamnati.
Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke ci gaba da kokarin inganta tsarin tattalin arzikin zamani, domin kara bunkasa kasuwanci, kirkire-kirkire, da samar da ayyukan yi ga matasa.
Korar Umunubo na iya zama wani bangare na sake fasalin shugabanci da gwamnati ke yi a wannan fanni, domin tabbatar da sahihancin wakilci da ingantaccen tsarin gudanarwa.
Haka kuma, sanarwar ta yi gargadin cewa kada wanda ya kuskura ya kulla wata mu’amala da tsohon hadimin shugaban kasar, domin ba ya daga cikin wakilan gwamnati.

Source: Twitter
Fadar shugaban ta gargadi jama'a kan Umunubo
Sanarwar ta ce:
"Muna sanar da daukacin jama’a cewa an tsige Fegho John Umunubo daga matsayin hadimin shugaban kan harkokin tattalin arzikin zamani da kirkire-kirkire (Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa)."
"Muna jan hankalin mutane su sani cewa daga yanzu bai shi da hurumin sake wakiltar wannan gwamnati a kowane irin matsayi.
"Daga yau duk wanda ya ci gaba da hulɗa da shi da sunan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, babu ruwanmu, shi ya jefa jansa a hadari.
"Muna fatan dukkan masu ruwa da tsaki da al’ummar fannin tattalin arzikin zamani da kirkire-kirkire za su dauki wannan sanarwa da muhimmanci."
Tinubu ya yi gyare-gyare a hukumar NCC
A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa kwamitin gudanarwa na Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da na asusun USPF.
Tinubu ya nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa wanda ke sa ido a hukumar NCC bayan ya rasa irin kujerar a UBEC.
A gefe guda kuma Ministan Sadarwa, Dr. Bosun Tijani, zai jagoranci kwamitin USPF, asusun da ke samar da kudin ayyukan sadawara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
