Kusan Watanni 2 bayan Ya Rasu, An Dauko Batun Ayyuka da Buhari Ya Gaza Yi a Arewa

Kusan Watanni 2 bayan Ya Rasu, An Dauko Batun Ayyuka da Buhari Ya Gaza Yi a Arewa

  • Dan gwagwarmaya daga jihar Kogi, Usman Okai Austin ya bayyana cewa har yanzu Arewa na bukatar samun ayyukan ci gaba
  • Usman ya caccaki tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan kin karisa ayyukan da Goodluck Jonathan ya faro a Arewa
  • Ya bayyana wasu mutane da ke sahun gaba a gwamnatin Buhari, yana mai cewa duka sun gaza yiwa Arewa abin da ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Ɗan gwagwarmayar siyasa kuma jigo a jam’iyyar PDP a jihar Kogi, Usman Okai Austin, ya soki tsohuwar gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.

Usman ya soki gwamnatin tsohon shugaban kasar ne bisa yadda ta gaza karasa ayyukan ci gaba da Goodluck Jonathan ya fara a yankin Arewacin Najeriya.

Jonathan sa Buhari.
Hoton Jonathan tare da Muhammadu Buhari lokacin da ya kai ziyara fadar shugaban kasa Hoto: @BashirAhmad
Source: Facebook

Matashin dan gwagwarmayar ya yi wannan suka ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi kwanan nan, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani bayan Tambuwal ya zargi Tinubu da shirin ruguza 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bar Arewa a baya ta fannin ci gaba

Usman Okai-Austin wanda ya nemi takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Dekina/Bassa a zaben 2023, ya ce ba abin da Arewa ta fi bukata kamar samun ci gaba.

Ya bayyana takaicin yadda matsalolin talauci, rashin tsaro, yara masu gararanba a titi suka mamaye Arewa duk da dogon lokacin da mutanen yankin suka yi a kan madafun iko.

"Arewa na bukatar ci gaba, ba mulkin siyasa mara amfani ba. Menene amfanin iko idan ba za ka rage wa mutanenka yunwa da talauci ba?
"Shin muna da asibitoci masu nagarta a Arewa? Muna da makarantu na zamani da aka tsara domin ’ya’yanmu? Amsar ita ce a'a,” in ji shi.

Okai ya soki gwamnatin Buhari kan wasu ayyuka

Usman Okai ya tuna yadda tsohon shugaban kasa Jonathan ya nuna kishin Arewa ta hanyar kafa makarantun tsangaya na zamani 157 don haɗa ilimin boko da na addini.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya tona asirin Kwankwasiyya, ya faɗi dalilin watsewa Kwankwaso

Sai dai ya zargi gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari da rashin ci gaba da irin wadannan ayyuka, inda ya ce an bar makarantu da dama sun lalace.

Ya kuma karyata maganar cewa gwamnati mai ci ta yi watsi da Arewa, yana mai cewa wasu ’yan siyasa ne kawai ke amfani da wannan batu don amfanin kansu.

Jigon PDP, Usman Okai Austin.
Hoton jigon PDP kuma dan gwagwarmaya a jihar Kogi, Usman Okai Austin Hoto: Usman Okai Austin
Source: Facebook

'Dan siyasar ya caccaki wasu mukarraban Buhari

Ya ambaci fitattun ’yan arewa da ke sahun gaba a gwamnatin Buhari kamar Nasir El-Rufai, Babachir Lawal, da Abubakar Malami, yana mai cewa sun samu damar kawo ci gaba amma suka gaza.

Sai dai El-Rufai bai yi aiki a gwamnatin tarayya ba a lokacin, ya yi mulkin jihar Kaduna, amma ana ganin yana da fada a wajen Buhari.

Usman Okai-Austin ya nuna damuwa kan zaman kashe wandon matasa, rashin tsarin kiwon lafiya mai nagarta ga mata, rashin tsaro da ya hana noma da yara masu yawo a toti.

'Dan gwagwarmayar ya bukaci canjin shugabanci, iya yi kira ga matasan Arewa su karɓi ragamar mulki daga tsofaffin shugabanni.

Me yasa Obasanjo ke sukar Buhari?

Kara karanta wannan

Yadda shugaba Tinubu ke yawan nadin mukamai ya warware daga baya

A wani labarin, kun ji cewa tsohon kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana abin da ya jawo alaka ta yi tsami tsakanin Muhammadu Buhari da Olusegun Obasanjo.

Ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya tsani Buhari ne kawai saboda ya gaza biya masa wata bukata da ya nema lokacin da yake kan mulki.

Garba Shehu ya ce marigayi tsohon shugaban kasar yana mutunta Obasanjo sosai, sai dai sun samu rashin jituwar ne kan wata buƙata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262