Yaron El Rufa'i: Uba Ya Yi Raddi ga Kalamai da Zarge Zargen Tsohon Gwamnan Kaduna

Yaron El Rufa'i: Uba Ya Yi Raddi ga Kalamai da Zarge Zargen Tsohon Gwamnan Kaduna

  • Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya yi martani ga Malam Nasir El-Rufai kan kalaman da ya yi game da shi
  • A lokuta da dama, tsohon Gwamnan, Nasir El-Rufa'i ya nanata cewa Uba yaronsa ne amma da alamar yanzu an ja layi
  • El-Rufai ya kuma yi zargin cewa gwamnatin Kaduna na biyan kudin fansa ga ’yan bindiga don a zauna lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya nuna cewa bai taɓa zama yaron Malam Nasir El-Rufa'i ba.

A cewar sa, manyan mutanen da suka yi tasiri wajen siyasarsa sun hada da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da marigayi babban lauyan kare haƙƙin ɗan Adam, Cif Gani Fawehinmi.

Kara karanta wannan

"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani ya fallasa 'yan siyasa kan matsalar rashin tsaro

Uba Sani ya yi martani ga El-Rufa'i
Hoton Nasir El-Rufa'i (H), Gwamna Uba Sani (Da) Hoto: Nasir El-Rufa'i/Uba Sani
Source: Twitter

A wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin TVC, Gwamna Uba ya ce ba ya jin ya dace ya rika mayar da martani kan batutuwan da ba su da amfani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya ƙaryata Nasir El-Rufa'i

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Uba Sani ya ce tun a shekarar 1994 ya hadu da Bola Tinubu a gidan Beko Ransome-Kuti

Ya ce ya kuma zauna a gidan Gani Fawehinmi lokacin gwagwarmayar kare hakkin dan Adam, don waɗannan mutane biyu su ne iyayen siyasarsa.

Ya ce yanzu burinsa shi ne samar da nagartaccen mulki ga mutanen Kaduna, ba rikon maganar mutane ko yin hayaniya da batutuwan da za su karkatar da shi daga aikin jama'a ba.

Uba Sani ya magantu kan biyan fansa

Gwamnan ya yi watsi da zargin da ake yadawa cewa gwamnatin sa tana biyan kudin fansa ga ’yan bindiga a yankunan da ke fama da rikici a jihar.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

Ya ce:

"Wannan ba gaskiya ba ne. Wasu ’yan siyasa na amfani da matsalar tsaro don samun tagomashi. Ba mu taba biyan ko kwabo ɗaya ba."

Ya bayyana cewa shawarwarin shugabannin al’umma kan amfani da dabarun lumana wajen kawo zaman lafiya na daga cikin abin da gwamnati ta yi amfani da shi ya kawo zaman lafiya, musamman a Birnin Gwari.

Dangane da rikicin da aka samu a wani taron jam’iyyar adawa a Kaduna kwanan nan, Gwamna Uba ya ce ba shi da hannu a lamarin.

Gwamnan jihar Kaduna ya ce ba ruwansu da harin ƴan adawa
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Ya kuma bukaci a bar rundunar ’yan sanda ta yi aikinta wajen gano hakikanin abin da ya faru.

Ya ce:

"An sha tsare ni sau biyar saboda kare dokar kasa. Ba zan taba shiga cikin wani abu da zai hana kowa ’yancin siyasarsa ba."

El-Rufa'i ya tsine wa gwamnatin Kaduna & APC

A baya, mun wallafa cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i, ya bayyana dalilinsa na sukar gwamnatin jihar a ƙarƙashin Gwamna Uba Sani.

Kara karanta wannan

Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci

Nasir El-Rufa'i ya kuma ce zai yi wuya gwamnatin Kaduna ta yi adalci a duk wani zaɓe da za a gudanar saboda Uba Sani ya sauka daga turbar da ya ɗora shi a kai.

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa a lokacin da yake mulki, gwamnatinsa ta gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci tare da ba ƴan adawa damar gudanar da ayyukansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng