Rikicin NNPP: Rigima Ta Barke a Jam'iyyar Kwankwaso bayan Korar sa Dan Majalisa a Kano

Rikicin NNPP: Rigima Ta Barke a Jam'iyyar Kwankwaso bayan Korar sa Dan Majalisa a Kano

  • Rikicin jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ya kara fitowa fili bayan korar dan Majalisar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin
  • Shugaban tsagin NNPP a jihar Kano, Sanata Jibrin Doguwa ya ce korar dan Majalisar ba ta inganta ba don ba shi da masaniya
  • Ya ce tsagin Kwankwasiyya da suka kori Jibrin Kofa ba su da hurumin daukar wannan mataki, ya yi barazanar kai kara kotu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Shugaban bangaren NNPP a jihar Kano, Sanata Jibrin Doguwa, ya yi watsi da sanarwar korar Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa daga jam’iyyar.

Doguwa ya bayyana cewa wannan mataki na korar Kofa daga NNPP ya saba doka, son haka ba sahihi ba ne.

Dan Majalisar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin.
Hoton Abdumimin Jibrin Kofa, dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji Hoto: Abdulmumin Jibrin
Source: Facebook

Shugaban tsagin NNPP a Kano ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Punch yau Asabar, 6 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Abdulmumin Jibrin ya yi martani kan korar da jam'iyyar NNPP ta yi masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kori Jibrin Kofa daga NNPP

Kalaman Doguwa na zuwa ne jim kadan bayan bangare da ke biyayya ga tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sanar da fattatakar Jibrin daga jam’iyyar NNPP

Shugaban bangaren Kwankwasiyya, Hashim Dungurawa, ya zargi Jibrin, dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji da cin amanar jam’iyya da kuma kin biyan hakkokin NNPP.

Sai dai da yake martani kan lamarin, shugaban tsagin NNPP reshen jihar Kano, Jibrin Doguwa ya ce wannan hukunci bai inganta ba.

An taso tsagin Kwankwaso a Kano

“Ni ne halastaccen shugaban jam’iyyar NNPP na Kano, an yanke wannan hukunci ne ba tare da saninmu ba, don haka ba shi da wani amfani, bai halatta ba,” in ji shi.

Ya kuma kare kalaman da dan Majalisar ya yi a hira da tashar Channels tv, wacce ta janyo ce-ce-ku-ce, inda ya ce ba ta saba wa muradun jam’iyyar NNPP ba.

Kara karanta wannan

"Yaudara ce": Gwamna Uba Sani ya fallasa 'yan siyasa kan matsalar rashin tsaro

“Abin da Kofa ya fada ba adawa da jam’iyya ba ne. Kowane ɗan siyasa yana da ’yancin canza jam’iyya. Shi kansa shugaban kasa Bola Tinubu ya taba canza jam’iyya kafin ya kai matsayin da yake a yau,” in ji Doguwa.
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa da Kwankwaso.
Hoton Abdulmumini Jibrin Kofa tare da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso Hoto: Abulmumin Kofa
Source: Twitter

Tsagin NNPP ya yi barazanar kai kara kotu

Ya zargi Dungurawa da yin abin da ya wuce huruminsa tare da yin barazanar daukar matakin kotu idan aka ci gaba da korar manyan jiga-jigan jam’iyyar NNPP.

“Idan Dungurawa bai daina wannan aikin nasa da ya saba doka ba, za mu hadu a kotu,” in ji shi.

Hon. Jibrin Kofa ya bar APC a shekarar 2022 tare da komawa NNPP karkashin inuwar Kwankwasiyya, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Safiyanu Aminu, dan Kwankwasiya a Kano ya shaida wa wakilin Legit Hausa cewa NNPP daya ce a Kano kuma Kwankwaso ne jagora.

A cewarsa, duk wadannan masu soki burutsun da sunan NNPP sun san wadanda ke daukar nauyinsu.

Safiyanu ya ce:

"Na ji dadi da jam'iyya ta kori Kofa kuma muna jiransa a 2027, yana daga cikin wadanda ni nake kallo a matsayin yan siyasar da ba su iya cin zabe sai sun jingina da wani."

Kara karanta wannan

Bayan katoɓararsa, NNPP ta kori Jibrin Kofa daga jam'iyyar, ta jero wasu dalilai

"Mu a NNPP ko Kwankwasiyya kanmu a hade yake, wadancan mun san wurin da muka ajiye su, yan neman tashin hankali ne kuma mun san masu daukar nauyinsu."

'Kwankwaso na iya sauya sheka zuwa APC'

A wani rahoton, kun ji cewa Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa ya sake jaddada cewa kofar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso bude take na komawa jam'iyyar APC.

'Dan Majalisar Wakilan ya ce har yanzu akwai damar hadewar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Kwankwaso, domin kofar jagoran NNPP a bude take ga duk mai so a tattauna.

Ya kara da cewa akidar Kwankwasiyya, wacce Kwankwaso ke jagoranta, tafiya ce mai ƙarfi wacce ba za a iya watsar da ita ba a lissafin siyasar ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262