Bayan Katoɓararsa, NNPP Ta Kori Jibrin Kofa daga Jam'iyya, Ta Jero Wasu Dalilai
- Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta sanar da korar Abdulmumin Jibrin daga jam'iyyar saboda zargin yin adawa da ita
- Shugaban jam’iyyar, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce nasarar Jibrin ta dogara ne da tallafin Kwankwasiyya da NNPP
- Dungurawa ya ce Jibrin ya ƙi biyan kudaden jam’iyya kuma za su gurfanar da shi a kotu don karɓar hakkinsu bisa doka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta dauki mataki mai tsauri kan dan majalisar tarayya daga jihar Kano.
Jam'iyyar ta tabbatar da korar Hon. Abdulmumin Jibrin, dan majalisar wakilai daga Kiru/Bebeji, bisa zargin adawa da jam’iyya da kuma kin biyan kudade.

Source: Twitter
Shugaban NNPP a Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya ce korar ta biyo bayan kalaman Jibrin a kafafen yada labarai kan jam’iyya da shugabancinta, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dalilin' da ya jawo korar Jibrin daga NNPP
Rahotanni sun nuna hakan na zuwa kwana guda bayan Jibrin ya ce ba abin mamaki ba ne idan ya fice daga jam’iyyar.
Ya kuma jaddada cewa yana da ikon yanke shawara da kansa kan abin da ya dace da shi a siyasa a kowane lokaci.
Hon. Jibrin Kofa ya kuma tabbatar da cewa babu abin da zai hana Bola Tinubu lashe zaben 2027 da ake tunkara a Najeriya.
Jam'iyyar NNPP ta tonawa Hon. Jibrin asiri
Dungurawa ya bayyana Jibrin a matsayin “dan siyasa mai rauni” da nasararsa ta dogara ne kacokan da Kwankwasiyya da kuma dandalin NNPP.
Sanarwar ta ce:
“Idan har yana da ƙarfi sosai da ya lashe zabe a karkashin APC, amma ya kasa, sai da NNPP ta tallafa masa."
Ya ce an kafa kwamiti domin duba hirar Jibrin da Channels TV, amma daga baya maganarsa ta nuna ya tsallake iyaka gaba ɗaya.
Ya ce:
“Maimakon tattaunawa, ya ci gaba da yin aiki akasin muradunmu, ya bayyana biyayyarsa ga wasu a waje, wannan ya sa muka kore shi."

Source: Facebook
Karin wasu zarge-zarge kan Hon. Jibrin
Dungurawa ya kuma ce Jibrin ya saɓa biyan kudaden jam’iyya da doka ta wajabta, inda suka kuduri aniyar gurfanar da shi a kotu.
“Za mu gurfanar da shi don dawo da abin da muke bin shi. Kowane mamba na da wajibin biyan kudin jam’iyya."
- In ji Dungurawa
Jam'iyyar NNPP ta bugi kirji kan karfinta
Game da jita-jitar komawarsa APC, Dungurawa ya ce hakan ba zai raunana NNPP ba, domin siyasa tana samun nasara ne da haɗin gwiwa, Tribune ta tabbatar.
Ya kara da cewa Kwankwasiyya na nan daram tare da jagoranta, Rabiu Musa Kwankwaso, kuma duk wani sauyi ba zai iya karya ƙarfinsu ba.
Kwankwaso: Hon. Jibrin ya fallasa 'yan APC
Kun ji cewa dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin ya yi magana kan siyasar Najeriya da zaben 2027.

Kara karanta wannan
"Ba laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano ya yi magana kan matsalar tsaron Arewa
Hon. Jibrin Kofa ya bayyana cewa wasu shugabannin APC a Kano ba sa son Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga jam’iyyar.
'Dan majalisar ya ce tattaunawa kan makomar siyasar Kwankwaso na ci gaba, amma ya fi mayar da hankali wajen samar da gwamnatin hadin guiwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

