Tambuwal Ya Yi Fallasa, Ya Tona Makircin Tinubu da APC kan 'Yan Adawa

Tambuwal Ya Yi Fallasa, Ya Tona Makircin Tinubu da APC kan 'Yan Adawa

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi maganganu na zargi kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC.
  • Aminu Tambuwal ya bayyana cewa rigingimun cikin gidan da suka addabi jam'iyyun adawa ba haka nan banza su ke faruwa ba
  • Sanatan ya bayyana cewa akwai hannun Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC wajen kunno rikicin da yake neman lakume jam'iyyun adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi zargi kan shugaban kasa Bola Tinubu da jam’iyyar APC.

Aminu Waziri Tambuwal ya zargi Tinubu da APC mai mulki da kunno wutar rikici a jam'iyyun adawa.

Tambuwal ya yi zargi kan Tinubu
Hoton tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Aminu Waziri Tambuwal, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Tambuwal ya yi wannan furuci ne a ranar Juma’a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane zargi Tambuwal ya yi kan Tinubu?

Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya ce APC da Tinubu sun tsara makircin karya gwiwar jam’iyyun adawa a kasar nan.

"Idan ka kalli abin da ke faruwa a cikin jam’iyyu daban-daban a Najeriya a yau, ba sai an gaya maka ba, duk yawan musun da za su yi ciki har da Shugaba Bola Tinubu, cewa ba su da hannu wajen lalata jam’iyyun adawa, ba gaskiya ba ne,”
"Ba wai ina zarginsu nake ba, amma ina cewa suna da hannu a kokarin da ake yi na lalata jam’iyyun adawa."

- Aminu Waziri Tambuwal

Lokacin da aka tambaye shi ya kawo hujjojin da ke goyon bayan wannan zargi, Tambuwal ya dage da cewa:

"Ina gaya muku, ba zargi nake yi ba. Suna da hannu a duk wannan lamari."

'Yan adawa na komawa jam'iyyar APC

An zaɓi Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023, inda ya doke tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP da sauran ‘yan takara.

Kara karanta wannan

Wike ko Atiku: Tambuwal ya fadi wanda zai marawa baya don zama shugaban kasa

Ko da yake waɗannan jam’iyyun sun samar da gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da ta jihohi, yawancin manyan shugabannin jam’iyyun adawa sun koma APC, abin da ya haifar da damuwa kan dimokuraɗiyyar kasar nan.

A ‘yan watannin nan, gwamnoni daga PDP, ‘yan majalisar LP da wasu daga jam’iyyu daban-daban sun fice daga jam’iyyunsu suka koma APC.

Tambuwal ya yi zargi kan Tinubu da APC
Hoton Aminu Waziri Tambuwal a majalisa da Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Aminu Waziri Tambuwal, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Haka kuma, wasu daga cikin jam’iyyun suna fama da rikice-rikicen cikin gida, abin da ya sa Tambuwal ya yi zargin cewa jam’iyyar APC mai mulki ce ke haddasawa.

Tambuwal ya ce zai marawa Atiku baya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana wanda zai iya marawa baya don zama shugaban kasa a tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike.

Tambuwal ya bayyana cewa gwara ya marawa Atiku baya kan Wike don zama shugaban kasa duk da abokantakar da ke tsakaninsu.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa dalilin da zai sa ya goyi bayan Atiku, shi ne saboda ya fi gamsuwa da cewa ya fi dacewa da jagorancin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng