'Dan Majalisar Tarayya na NNPP na Iya Ficewa daga Tafiyar Kwankwaso a Kano
- Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kiru da Bebeji, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya ce da yiwuwar ya fice daga NNPP ko ya ci gaba da zama
- Kofa dai na daya daga cikin 'yan tafiyar Kwankwasiyya da ake ganin suna da kusanci da jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso
- Ya ce ko da ya bar NNPP ba zai taba zagi ko cin mutuncin Kwankwaso ba domin ba halinsa ba ne kuma ya san cewa Kwankwasiyya ta taimake shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Hon. Abdulmumin Jibrin, dan majalisa mai wakiltar Kiru/Bebeji kuma na kusa na jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce da yiwuwar ya canza jam'iyya.
'Dan Majalisar Wakilan, wanda aka fi sani da Kofa ya ce shekaru da gogewar da yake da su, sun isa ya yanke shawara kan abin da ya fi dacewa da shi a siyasa.

Source: Twitter
Kofa ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da DCL Hausa, wacce aka wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kofa ya amince Kwankwasiyya ta taimake shi
'Dan majalisar ya ce ya shiga tafiyar Kwankwasiyya da rufin asirinsa, yana mai cewa babu shakka NNPP ta taimaka masa wajen komawa Majalisar Wakilai a 2023.
"Ita kanta jam’iyyar NNPP ta ce kofarta a bude take ta tattauna da sauran jam’iyyu, don haka ba lallai bane sai na bi dukkan abin da jam’iyya ta ce.
“Ina kara gode wa Allah amma shekaru na sun kai yadda zan yanke shawara kan abin da ya fi dacewa da ni,” in ji shi.
'Dan Majalisar zai bar Kwankwaso gaba daya?
Sai dai Jibrin ya kara da cewa, zai ci gaba da girmama Kwankwaso a matsayin jagora, ko da kuwa ba su kasance a jam’iyya daya ba.

Kara karanta wannan
"Ba laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano ya yi magana kan matsalar tsaron Arewa
“Ko da ban kasance tare da Kwankwaso ba, ba zan taba cin mutuncinsa ba kuma dama kowa ya san ba hali na ba ne, ban taba zagin Ganduje ba duk da irin rabuwar da muka yi balle kuma Kwankwaso."
- Abdulmumin Jibrin.
Ya kuma bayyana cewa bai taba neman kwangila ba duk da rawar da ya taka wajen nasarar NNPP a Kano, yana mai cewa, “Kwankwasiyya ta taimaka min, amma ni ma na tsaya mata,"

Source: Facebook
Shin Abdulmumin Jibrin zai fice daga NNPP?
Da aka tambaye shi ko zai bar jam’iyyar NNPP, Abdulmumini Jibrin ya ce:
“Komai zai iya faruwa, zan iya ci gaba da zama a NNPP, zan iya fita daga NNPP idan na ga dama na koma APC, idan na ga dama na koma PDP ko ADC ko PRP.
"Duk lokacin da na yanke hukunci za ku ji, shekaru na sun kai na yanke shawara kan abin da ya shafi makomar siyasata."
Duk da yana jam’iyyar NNPP, ana ganin Abdulmumin Jibrin na da kusanci sosai da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, cewar rahoton Daily Trust.
'Dan Majalisar NNPP ya hango nasarar Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Abdulmumini Jibrin Kofa ya bayyana cewa babu abin da zai iya dakatar da Shugaba Tinubu daga lashe zaben 2027.
'Dan Majalisar ya tabbatar da cewa yana tare da Bola Tinibu kuma a iya hasashensa, shugaban kasa zai yi tazarce zuwa zango na biyu.
Hon. Jibrin Kofa ya kuma kara da cewa akwai bukatar yankin Kudu ya kamata ya kammala shekaru takwas a mulki, don adalci tsakanin bangarorin kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

