2027: Makusancin Kwankwaso Ya Hango wa Tinubu Matsala idan aka yi Watsi da Kashim
- 'Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji a Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ba shugaba Bola Tinubu shawara
- Ya ce batun sauya Kashin Shettima a zaben 2027 zai jawo wa Shugaban Kasar matsala shigen wanda ta taso a shekarar 2023
- Kalaman Jibrin Kofa na zuwa ne a lokacin da ake hasashen tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso zai iya koma wa APC
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi magana ka zaben 2027.
Ya kuma bai wa Shugaban Kasa, Bola Tinubu shawara a kan batun ajiye Kashim Shettima a kakar zaben da ke tunkaro 'yan Najeriya.

Source: Facebook
A hirarsa da Channels TV, 'Dan Majalisar ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu zai iya tafka kuskure ko ya yi kwaba idan ya ajiye Kashim Shettima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Jibrin ya yi kira ga Tinubu
The Guardian ta wallafa cewa Hon AbdulMumin Jibrin Kofa ya nemi Tinubu ya ci gaba da tafiya da mataimakinsa Kashim Shettima idan zai tsaya takara a wa’adin biyu.
A cewarsa, neman wani mataimakin shugaban ƙasa daga Arewa zai iya haifar da rudani da saɓani irin na zaben 2023.

Source: Facebook
'Dan Majalisar, wanda ke cikin jam’iyyar NNPP, ya ce masu ba wa shugaban ƙasa shawarar neman wani mataimaki ba sa son shi da alheri.
Ya kara da cewa gwamnati ta samu nasarori, ciki har da cimma burin tara kuɗin shiga, wanda hakan ya kawar da bukatar neman bashi a cikin Najeriya.
Hon. Kofa ya jinjina wa shugba Tinubu
A kalamansa, 'dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP a jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce bai dace a rika ganin laifin Bola Tinubu a kan wasu abubuwa ba.

Kara karanta wannan
"Ba laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano ya yi magana kan matsalar tsaron Arewa
Hon. Kofa ya ce:
“Ba adalci ba ne a jingina matsalolin tsaro kai tsaye ga Shugaba Tinubu. Ya gaji gwamnati da matsalolin da suka tara shekaru 60 baya, don haka ba gaskiya ba ne a ɗora wa wanda bai shekara biyu a mulki laifin dukkannin matsalolin tattalin arziki da tsaro ba."
Ya kara da cewa ya san shugaban yana aiki tukuru domin ganin cewa an magance matsalolin da su ka taso Najeriya a gaba.
Kofa ya yi magana kan shirin 2027
A wani labarin, kun ji cewa Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ya damuwa da shirin taron dangi da wasu ‘yan Arewa ke yi kafin zaben 2027.
A cewar Hon Kofa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kallon shirin da wasu ke yi na kifar da shi a matsayin abin dariya, ganin yadda Arewa ke da rikici da sabani a cikinta.
Ya ce babbar matsalar Arewa ita ce rashin haɗin kai tsakanin shugabanninta, abin da ya sanya shugaba Tinubu ya fi karkata wajen mayar da hankali ga nasarorin da gwamnatinsa ke samu.
Asali: Legit.ng
