2027: 'Dan Kwankwasiyya Ya Raba Gardama kan Batun 'Yan Arewa ba Sa Tare da Tinubu

2027: 'Dan Kwankwasiyya Ya Raba Gardama kan Batun 'Yan Arewa ba Sa Tare da Tinubu

  • 'Dan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Kano, Abdulmumin Jibrin, ya yi magana kan tasirin mai girma Bola Tinubu a Arewacin Najeriya
  • Abdulmumin Jibrin ya aminta da cewa tabbas akwai mutanen da ke adawa da Shugaba Tinubu a yankin Arewa
  • Sai dai, ya nuna cewa kuskure ne babba a yi tunanin cewa shugaban kasan bai da mutanen da ke goyon bayansa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya yi magana kan goyon bayan siyasa da Shugaba Bola Tinubu yake da shi a Arewa.

Abdulmumin Jibrin ya karyata ikirarin da ke cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da goyon bayan siyasa a Arewacin Najeriya.

Abdulmumin ya ce Tinubu na da magoya baya a Arewa
Hoton shugaban kasa Bola Tinubu da Abdulmumin Jibrin Kofa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Abdulmumin Jibrin
Source: Facebook

Dan majalisar na jam'iyyar NNPP ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Laraba, 3 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu na da magoya baya a Arewa

Abdulmumin Jibrin ya jaddada cewa har yanzu shugaban kasa na da karfin magoya baya a yankin Arewacin Najeriya.

Jigon na jam’iyyar NNPP ya ce "lissafi ne mai hadari” a yi tunanin cewa shugaban kasa ba shi da goyon baya a Arewa.

Ya jaddada cewa duk da cewa akwai wadanda ke adawa da shi, akwai da dama da ke goyon bayansa.

“Tinubu ba maraya ba ne a Arewa. Yana da jama’a a Arewa. Wata kila ba sa magana yadda ya kamata, amma yana da mutane. Don haka, kamar yadda ake da wadanda ke son a kore shi, haka ma akwai wadanda ke son ya ci gaba da zama."
"Kuma yayin da abubuwa ke ci gaba da faruwa, za ku ga mutane da za su fito suna adawa, da kuma wadanda za su fito suna goyon bayansa. Saboda haka ban yarda cewa shi maraya ba ne a Arewa."

Kara karanta wannan

"Ba laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano ya yi magana kan matsalar tsaron Arewa

"Babban kuskuren lissafi ne ga wani ya yi tunanin Tinubu ba shi da goyon baya a Arewacin Najeriya."

- Abdulmumin Jibrin Kofa

Dan Kwankwasiyyan ya ba Arewa shawara

'Dan majalisar wakilan ya kuma karyata zancen cewa Arewa ta koma baya a siyasa, yana mai nuna cewa yankin ya rike mulki fiye da Kudu.

Abdulmumin Jibrin ya ba Arewa shawara
Hoton dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin Kofa Hoto: Abdulmumin Jibrin
Source: Facebook

Ya shawarci Arewa da ta “fadawa kanta gaskiya” kuma ta daina batawa wakilanta suna.

Wadannan kalaman na sa sun fito ne a daidai lokacin da ake ta maganganun siyasa gabanin zaben 2027.

Sai dai kasa da shekaru biyu kafin zaben, ‘yan adawa sun kafa hadaka da ta hada da fitattun mutane irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, da Dino Melaye.

Jibrin ya magantu kan komawar Kwankwaso APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya yi magana kan yiwuwar Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC.

Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa a shirye madugun na Kwankwasiyya yake wajen komawa jam'iyya mai mulki.

Dan majalisar ya bayyana cewa har yanzu akwai damar yin aiki tare tsakanin Kwankwaso da mai girma Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng