Jibrin Kofa: Na Kusa da Kwankwaso Ya Fadi Matsalar Arewa a Shirin Kifar da Tinubu a 2027

Jibrin Kofa: Na Kusa da Kwankwaso Ya Fadi Matsalar Arewa a Shirin Kifar da Tinubu a 2027

  • Abdulmumin Jibrin ya yi maganganu kan batun tazarcen Mai girma Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027
  • Dan majalisar wanda yake na kusa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna cewa yankin Arewa na da matsaloli gabanin zaben 2027
  • Ya bayyana cewa shugaban kasa Tinubu zai rika jin dadin wasu abubuwan da ke faruwa a fagen siyasar Arewacin Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Makusancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi magana kan tazarcen mai girma Bola Ahmed Tinubu.

Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa Shugaba Tinubu bai damu da batun taron dangi da Arewa ke shirin yi masa ba kafin zaben 2027.

Abdulmumin Jibrin ya kare Shugaba Tinubu
Hoton Abdulmumin Jibrin tarr da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru/Bebeji ta jihar Kano a karkashin NNPP, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels Tv a ranar Laraba, 3 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

"Ba laifin Tinubu ba ne," Dan Majalisa daga Kano ya yi magana kan matsalar tsaron Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace matsala yankin Arewa ke da ita?

Abdulmumin Jibrin ya ce rashin hadin kan shugabannin Arewa ne zai sanya Shugaba Tinubu zai ki damuwa da batun yi masa taron dangi kafin zaben 2027.

Ya bayyana cewa nuna kamar Arewa ta hada kai gaba daya kan adawa da Tinubu yaudara ce.

"Ga wadanda ke cewa za su kayar da shi, lallai yana zaune a wani wuri yana dariya saboda yana ganin yadda muke da sabani a tsakaninmu."
"Haka ma kuskure ne a nuna kamar Arewa ta hade gaba daya a kansa. Shi ba maraya ba ne a Arewa."
“Idan ka ce akwai wani taron dangi ko Arewa ta hada kai, ya kamata mu daina yaudarar kanmu. Arewa kullum tana adawa da kanta. Ina hadin kan? Abin da muka saba yi shi ne hada kai don rushe duk wanda ya fito daga yankin. Wannan shi ne abin da ke faruwa kullum."

Kara karanta wannan

Farashin Dala: Bincike ya karyata ikirarin Tinubu kan farfado da darajar Naira

- Abdulmumin Jibrin Kofa

Abdulmumin ya koka da rashin hadin kan Arewa

Dan majalisar, wanda ya hadu da Tinubu sau biyu a cikin makonnin da suka gabata, ya ce duk da yawan jama’a da kuma wadatar albarkatu da Arewa ke da su, rashin jituwa a tsakaninta ya raunana tasirinta.

“Kullum muna yin fada da juna a talabijin na kasa. Shin wai Arewa ba ta da shugabanni? Sarakunan gargajiya fa? Gwamnonin Arewa guda 19 fa? Su waye za mu kira shugabanninmu idan suna yi wa juna kazafi a idon jama’a?"

- Abdulmumin Jibrin Kofa

Abdulmumin Jibrin ya koka kan halayyar Arewa
Hoton Abdulmumin Jibrin tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Abdulmumin Jibrin
Source: Twitter

Dan majalisar ya kuma jaddada cewa yankin Kudu na da hakkin kammala shekaru takwas bayan wa’adin mulki biyu na marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Abdulmumin ya hango nasarar Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya yi hasashe kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

'Dan Kwankwasiyya ya yi ta maza, ya zaɓi wanda ya fi so tsakanin Kwankwaso da Tinubu

Abdulmumin Jibrin Kofa ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai sake darewa kan kujerarsa a wa'adi na biyu.

Dan majalisar na jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa a ganinsa babu wani abu da zai kawo cikas a tazarcen mai girma Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng