An Fasa Ƙwai: Hon. Jibrin Ya Fallasa Waɗanda ba Su Son Kwankwaso Ya Shiga APC
- Dan majalisar tarayya daga jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin ya yi magana kan siyasar Najeriya da zaben 2027
- Hon. Jibrin ya bayyana cewa wasu shugabannin APC a Kano ba sa son Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga jam’iyyar
- Ya ce tattaunawa kan makomar siyasar Kwankwaso na ci gaba, amma ya fi mayar da hankali wajen samar da daidaito da gwamnati
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Dan majalisar tarayya daga jihar Kano. Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya yi wasu maganganu kan siyasar jihar.
Hon. Jibrin ya bayyana cewa shi dan NNPP ne amma kuma yana tare da Bola Tinubu tare da yi masa fatan nasara a 2027.

Source: Twitter
Jibrin, wanda ke wakiltar Kiru/Bebeji a ƙarƙashin NNPP, ya faɗi haka ne ranar Laraba a shirin Politics Today na tashar Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ganawar Jibrin Kofa da Tinubu ta jawo zargi
A ranar 11 ga Agustan shekarar 2025, Jibrin ya gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa, Abuja, karo na biyu cikin sati biyu.
Jibrin ya ƙi bayyana manufar ganawar ga manema labarai, amma ya ce “komai a buɗe yake” tare da jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya.
Ya ƙara da cewa abu mafi muhimmanci shi ne daidaiton ƙasa da haɗin kanta inda ya ce idan aka kai ga haka, za a ci nasara.

Source: Twitter
Kofa ya magantu kan rashin shigan Kwankwaso APC
Jibrin dai na da alaƙa ta siyasa mai ƙarfi da shugaba Bola Tinubu da kuma tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.
Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin APC a jihar ba sa son Kwankwaso shiga jam’iyyar.
'Dan majalisar ya bayyana makomar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso musamman ganin ana ta jita-jitar zai koma APC.

Kara karanta wannan
2027: Makusancin Kwankwaso ya hango wa Tinubu matsala idan aka yi watsi da Kashim
Hon. Kofa ya ce:
“In ka ce Kwankwaso yana shirin shiga APC, akwai mutane da dama a APC Kano da ba sa son hakan saboda manufofin siyasa."
Burin Jibrin Kofa a siyasar Kano da Najeriya
Ya ce tattaunawa kan hanyar siyasar Kwankwaso tana ci gaba, amma shi kansa yana maida hankali wajen samar da daidaito da gwamnati ta haɗin kai.
“Ina ƙoƙarin ganin cewa, saboda Kano da Najeriya, akwai daidaito a siyasa, hanya ce mai matuƙar rikitarwa.
“Tun farko na ke cewa mu yi aiki tare da gwamnati ta haɗin kan ƙasa, wannan ra’ayi nawa ya dade."
- Cewar shi
Ya ƙara da cewa Kwankwaso har yanzu a shirye yake ya shiga APC, tare da bude kofa ga duk wata tattaunawa kan siyasa.
Hon. Kofa ya kare Tinubu kan matsalar tsaro
A baya, mun kawo muku cewa Dan Majalisar Wakilai daga Kano, Hon. Abdulmumini Jibrin ya kare Bola Tinubu kan matsalar tsaro.
Kofa ya ce bai kamata a dorawa Shugaba Tinubu laifin matsalar tsaron Arewa ba duba da kokarin da yake yi.
Jibrin Kofa daga NNPP ya ce Tinubu ya tara yan adawa a Arewa da Kudancin Najeriya wanda hakan ke kara zama masa kalubale.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
