'Kwankwaso Ya Bude Kofa, da Yiwuwar Ya Hade da Shugaba Tinubu a APC kafin 2027'

'Kwankwaso Ya Bude Kofa, da Yiwuwar Ya Hade da Shugaba Tinubu a APC kafin 2027'

  • Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa ya sake jaddada cewa kofar jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso bude take na komawa APC
  • 'Dan Majalisar Wakilan ya ce ba abin mamaki ba ne Kwankwaso da Shugaba Tinubu su koma inuwa daya kafin zaben 2027
  • Abdulmumini Kofa ya sha kai wa Tinubu ziyara a baya-bayan nan, lamarin da ya sa ake rade-radin yana shirin ficewa daga NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - 'Dan Majalisar Wakilan Tarayya daga Kano, Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa ya dawo da batun hadewar Rabiu Kwankwaso da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Hon. Kofa ya bayyana cewa jagoran NNPP na kasa, Dr. Rabiu Kwankwaso a shirye yake ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Abdulmumini Kofa tare da Bola Tinubu.
Hoton Abdulmumini Kofa tare da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

'Dan Majalisar, wanda yana daya daga cikin na hannun daman Kwankwaso, ya fadi haka ne a cikin shirin Politics Today na tashar Channels tv yau Laraba.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Rigima ta barke a jam'iyyar Kwankwaso bayan korar da dan Majalisa a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kofa ya budewa Kwankwaso kofar tattaunawa

Jibrin Kofa ya ce har yanzu akwai damar hadewar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da Kwankwaso, domin kofar jagoran NNPP a bude take ga duk mai so a tattauna.

"Game da batun komawa APC, a iya abin da na sani har yanzu kofar Kwankwaso a bude take, mun shirya tattauna wa da kowace jam'iyya, ba abin da ba zai iya yiwuwa ba."

- In ji Hon. Abdulmumini Jibrin Kofa.

A watannin bayan, an yada jita-jitar cewa da yiwuwar Kwankwaso ya koma APC kafin zaben 2027, wasu ma na ganin Tinubu na shirin daukarsa a matsayin abokin takara.

Kodayake maganar kamar ta lafa a yan kwanakin nan, amma Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa Kwankwaso ya bude kofar tattaunawa ga kowa.

Kwankwaso zai iya komawa APC kafin 2027?

Da aka tambaye shi abin da ka iya jawo jinkirin shigar Kwankwaso APC, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Gidaje da Muhalli ya ce:

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Tarayya na NNPP na iya ficewa daga tafiyar Kwankwaso a Kano

“Ko a cikin APC ta Kano, akwai masu muradun kansu da ba za su so mu shiga ba, wata kila saboda burin zama gwamna ko wasu dalilai na siyasa," in ji Kofa.

Ya kara da cewa akidar Kwankwasiyya, wacce Kwankwaso ke jagoranta, tafiya ce mai ƙarfi wacce ba za a iya watsar da ita ba a lissafin siyasar ƙasar nan.

An sha ganin Jibrin yana ziyartar Shugaba Tinubu sau da dama, hakan ya jawo jita-jitar cewa zai iya barin NNPP.

Hon. Kofa tare da Kwankwaso.
Hoton dan Majalisar Kiru da Bebeji, Hon. Abddulmumini Jibrin Kofa da Kwankwaso Hoto: @SaifulllahiHon
Source: Twitter

Abdulmumini Kofa na shirin komawa APC?

Sai dai har yanzu dan Majalisar bai tabbatar da jita-jitar ko ya musanta ba, sai dai da aka tambaye shi, ya jaddada cewa, "zan ci gaba da maimaita abin da fada ne a baya, komai na iya faruwa."

Ya bayyana cewa ko da yake shi ɗan Kwankwasiyya ne, hakan ba yana nufin sai ya nemi izinin Kwankwaso kafin ya bar NNPP ba.

“A’a, a shekaruna na yanzu, ina da ikon yanke hukunci da kaina,” in ji shi Hon. Kofa, wanda ke wakiltar Kiru/Bebeji a Majalisar Wakilai.

Wani dan Kwankwasiyya ya shaida wa Legit Hausa cewa ba ya tunanin jagoransu zai bar NNPP zuwa wata jam'iyya kafin zaben 2027.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya tona asirin Kwankwasiyya, ya faɗi dalilin watsewa Kwankwaso

Sa'idu Abdullahi ya bayyana cewa a shirye suke su amsa kiran Kwankwaso duk inda ya bukaci su koma, amma dai sun fi son ya sake neman takara a zabe na gaba.

"Mun yarda da maigida, duk inda ya ce mu koma za mu tafi ba tare da jayayya ba. Mu ko a haka aka tsaya mun san Kwankwaso na da kima a siyasa, tun da shugaban kasa da kansa na son aiki da shi," in ji shi.

Kwankwaso ya hango shirin 'yan Najeriya a 2027

A wani labarin, kun ji cewa madugun Kwankwasiyya ya bayyana cewa galibin 'yan Najeriya sun riga sun kudirta abin da za su yi a zaben 2027.

Kwankwaso ya ce yunwa da tsananin talauci sun hana miliyoyin ‘yan Najeriya sukuni da walwala, wanda yake ganin za su yi tasiri zaben da ke tafe.

Ya ce matsalolin da al’umma ke fuskanta sun nuna cewa jama’a sun gama yanke shawara, inda ya tabbatar da cewa NNPP ce ke tare da talakawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262