Kusa a APC Ya 'Tabbatar' da Tazarcen Tinubu, Ya Ce a Jira 2027

Kusa a APC Ya 'Tabbatar' da Tazarcen Tinubu, Ya Ce a Jira 2027

  • Babba a jam'iyyar APC, Farouk Adamu Aliyu ya yi watsi da barazanar adawa yana mai cewa jam’iyya za ta ci gaba da riƙe madafun iko
  • A ikirarin da ya yi, ya bayyana cewa babu wani abu da zai iya hana Bola Ahmed Tinubu koma wa kujerar shugabancin Najeriya a 2027
  • Ya ce matsalolin da ake ta kumfar baki a kansu a yau, ba matsala ce da ta kebanta da Shugaban Kasa kadai ba, har da sauran 'yan kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Babban jigon jam’iyyar APC mai mulki, Farouk Adamu Aliyu, ya bayyana cewa babu abin da zai hana Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sake lashe zaɓe a 2027.

Farouq Aliyu ya yi wannan bayani ne ranar Talata yayin da yake amsa tambayoyi a kan salon mulkin Shugaban Kasa da kuma hasashen makomar APC a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin baiwa jihar Legas fifiko wajen ayyukan raya kasa

Jigon APC ya ce Tinubu zai koma mulki
Hoton Shugaban Kasa, Bola Tinubu cike da farin ciki Hoto: Ajuri Ngalale
Source: Facebook

Babba a APC ya kare Bola Tinubu

Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Farouk Adamu Aliyu ya bayyana cewa duk wata barazanar 'yan adawa ba za ta kawo cikas ga komawarsa Aso villa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, akwai abubuwa da dama da ke cin karo da gaskiya, inda yawanci matsalolin da ake jingina wa ga Shugaban Kasa bai dace ba.

Ya ce:

“Ina so ku fahimci cewa akwai wasu abubuwa da ba za mu yi ba. Haka kuma gaskiya ne cewa idan mutum ya zama shugaban ƙasa, akwai wasu abubuwa da bai kamata ya yi ba.
“Kowace irin matsala da ake fuskanta a ƙasar nan, ana jingina shi kai tsaye ga shugaban ƙasa. Amma gaskiyar magana, bari in faɗi, akwai wasu abubuwan da muka taɓa jingina wa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan da ba su dace ba.

Tinubu zai dawo 2027 Inji Jagoran APC

Faruk Adamu Aliyu ya ƙara da cewa wannan yanayin na matsaloli da kalubalen 'yan adawa ba za su hana Tinubu samun nasara a zaɓen 2027 ba.

Kara karanta wannan

"Ana yiwa Arewa aiki," Musa Kwankwaso ya hango manyan 'yan adawa za su koma APC

Jigon APC ya ce 'yan adawa na kokarin kawar da gwamnati
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A kalamansa:

“Bari in gaya muku, babu wani abu da zai iya hana Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu sake dawowa kan karagar mulki a shekarar 2027."

A cewar 'dan siyasar, jam’iyyar na da tabbacin ci gaba da riƙe madafun iko saboda kwarewar shugabancin Tinubu da kuma irin rawar da ya taka wajen gyaran tsarin tattalin arzikin ƙasar da gina dimokuraɗiyya.

Fadar Shugaban kasa ta kare Bola Tinubu

A wani labarin, mun wallafa cewa Mai ba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana Jihar Legas a matsayin “ƙasar kowa."

Ya ce wannan dalili ne ya sa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta zage tana ruwan manyan ayyukan raya kasa da kawo ci gaban tattalin arziki a jihar domin kowa ya mora.

Ya ce matsayin jihar Legas ba daya ya ke da na sauran jihohin kasar nan, musamman ta fuskar bunkasa tattalin arziki da kawo wa kasa abubuwan alheri a lokuta daban daban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng